Yadda Buhari ya yi fama da cutar kaduwa sakamakon yakin basasa

Mai dakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bayyana yadda shugaban ya yi fama da cutar kaduwa sakamakon yakin basasar da aka yi a kasar a shekarar 1967 zuwa 1970. Buhari ya fafata a yakin basasar ne lokacin yana sojan Najeriya. Aisha Buhari ta bayyana haka ne ranar Talata yayin da kungiyar matan manyan sojoji da manyan 'yan sanda ta kasar, ta kaddamar da cibiyar kula da samar da magani ga dakarun da suka kamu da lalurar damuwa a fagen daga a lokacin da suke kan aiki. Akwai cibiyoyi na kula da lafiyar dakarun da suka samu raunuka a fagen daga a Najeriya, sai dai wannan shi ne karon farko da aka samar da cibiyar da za ta kula da wadanda suka samu tabin hankali da damuwa mai tsanaki.

Aisha Buhari ce babbar bakuwa a taron sanya tubalin ginin cibiyar wadda a turanci ake kiran matsalar PTSD, wato Post-Traumatic Stress Disorder.

Cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai babban hafsan sojojin Najeriya Janar Lucky Irabor da Laftan-Janar Farouk Yahaya, hafsan hafsoshin sojojin kasa da mataimakin shugaban kasar Laberiya Jewel Howard Taylor da tsohuwar shugabar kasar Malawi Joyce Banda da kuma 'yar majalisar dattawan Birtaniya Baroness Sandy Verma.

Aisha Buhari ta ce duk da cewa saura wata bakwai wa'adin mulkin maigidanta ya kare, gwamnatinsa za ta kammala ginin cibiyar wadda za ta sami mazauninta a Abuja.

Aisha Buhari ta kuma sanar da jama'ar da suka halarci bikin cewa Shugaba Buhari ma ya yi fama da lalurar damuwa na shekaru masu yawa saboda rawar da ya taka a yakin basasan kasar da hamabarar da gwamnatinsa da aka yi da kuma tsare shi da aka yi na watanni 40 ba tare da an caje shi da aikata wani laifi ba.

Ta bayyana yadda matsalar damuwar ta shafi aurenta, a daidai lokacin da ta ke sabuwar amarya.

"Gaskiya ce sojoji da iyalansu na rayuwa cikin wannan yanayi na damuwa, musamman tasirinsa maras kyau. Kasancewa ta matar soja ko matar sojan da ya ajiye aiki, kuma ga shi na kasance mai kwarewa kan kiwon lafiyar jiki, lallai na fahimci irin kalubalen da ke tattare da lalurar PTSD da yadda take shafar iyalan sojoji da ma kasa," in ji ta.

Ta kuma ce mijinta ya yi aikin soji na shekau 27 gabanin a hambarar da gwamnatinsa yayin wani juyin mulki.

Aisha Buhari ta ce: "Yana cikin sojojin da suka gwabza yakin basasa na watanni 30 kuma babu wani matakin kula da kiwon lafiyarsa da aka dauka; sannan ya ya mulki kasar na watanni 20 amma bayan haka an tsare shi na tsawon watanni 40 ba tare da an sanar da shi laifin da ya aikata ba."

Ta ce shekara guda bayan da aka sako shi daga inda ake tsare da shi ne aka daura mata aure da shi.

"Na shafe shekaru 19 ina zaune da shi a matsayin matarsa, kuma ni ma wannan matsalar ta PTSD ta shafe ni, a matsayina na mace mai shekaru 19 kawai, a ce na dauki nauyin kulawa da mutumin da ya rike mukamin shugaban kasa da kwamandan sojojin Najeriya, ka ce masa bai yi daidai ba shi ne kuskure na farko da za ka iya yi."

Ta ce: "Saboda haka ne ya zama min tilas na nemi hanyar da zan fahimtar da shi domin guje wa zama mai laifi. Musamman idan aka yi la'akari da yadda ya tsaya takara a zabukan 2003 kuma ya fadi zabe, da na 2007 da na 2011 - dukkansu kuma bai yi nasara ba - wanda wannan ya mayar da ni tamkar wata malamar asibiti mai kula da lafiyar kwakwalwa."

Ta kara da cewa: "Ku yi tunanin yadda tun ina mai shekaru 19 nake tare da mutumin da ya gwabza yakin basasa kuma aka yi masa juyin mulki sannan ya fadi zabuka uku a jere sannan daga baya ya sami shiga fadar shugaban kasa a 2015. Sannan bai dace mace ta sanar da su cewa abu kaza bai dace ba ko abu kaza ya dace, musamman a Najeriya da Afirka, ana kallon irin wannan a a matsayin babbar matsala."