Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Majalisar Amurka ta amince da tallafin dala biliyan 95 ga Ukraine da Isra'ila
Majalisun dokokin Amurka sun amince da gagarumin tallafi na waje da aka dade ana jira, wanda ya kunshi tallafin yaki ga Ukraine da Isra’ila.
Kudurin doka guda hudu da majalisar wakilai ta amince da su a karshen mako, a yanzu sun samu amincewar majalisar dattawan Amurkar da gagarumin rinjaye daga bangare biyu na majalisar - ‘yan Republican da kuma ‘yan Democrat.
Wannan wani muhimmin lokaci ne ga Amurka – bayan wata da watanni na rashin tabbas – tare da rashin samun goyon baya daga ‘yan Republican wadanda ke nuna tababa da kin yarda da yadda Amurka ke shiga yake-yake na kasashen waje.
A karshe dai kai ya hadu murya ta zo daya- ‘yan majalisun sun amince da wannan tallafi na dala miliyan dubu 95 ga Ukraine da Isra’ila da kuma taiwan.
Jagoran majalisar, dan Democrat , Chuck Schumer ya ce , wannan mataki nasu ya gaya wa makiyan Amurka cewa fa kada su yi wasa da su. – Amurka za ta yi duk abin da za ta iya a cewarsa domin kare dumukuradiiyya.
Ya kara da cewa Amurka ta nuna wa kawayenta ba za ta taba juya musu baya ba.
Su kuwa ‘yan Republican marassa rinjaye a majalisar, jagoransu Mitch McConnell cewa ya yi rana ce mai muhimmanci sosai ga Amurka da kuma duniya mai ‘yanci.
Ya kara da cewa : ''Tsawon watanni abokanmu sun zuba ido su ga ko har yanzu Amurka tana da karfin da ta yi nasara a yakin cacar baka, ko kudurin kare zaman lafiya da yalwa tsawon gomman shekaru.''
Daga cikin kudin tallafin akwai dala bliyan 61 ga Ukraine da Shugaba Biden ya ce Ukraine na matukar bukata domin samar da garkuwa ta sama a yakin da kasar ke yi da Rasha.
Ita kuwa Isra’ila za ta samu karin tallafi na yakin da take yi da kuma tallafi ga mutanen Gaza dala biliyan 26.
Tallafin kasashen wajen na Amurka ya kuma kunshi tanadin da zai kai ga haramta amfani da shafin sada zumunta da muhawara na TikTok a Amurkar.
Idan masu shafin ‘yan China suka ki sayar da shi cikin shekara daya.
Gwamnatin Amurka na nuna damuwa gwamnatin China za ta iya amfani da shafin wajen samun bayanai na Amurkawa da ke amfani da shafin a don haka ne ta ce ta kafa wa shafin kahon zuka.
Masu kamfanin shafin na TikTok sun musanta dukkanin zargin da Amurka ke musu da kuma cewa za su kalubalanci matakin a kotu.