Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya ta kora mutane wurin da aka binne bama-bamai a Sudan ta Kudu
- Marubuci, Christina Simons
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai ɗaukar hoto daga Sudan ta Kudu
Wata mummunar ambaliyar ruwan da ba a taba ganin irinta ba a cikin shekara fiye da 50, da ta shanye gefen Kogin Nilu a bara, ta sa dubban 'yan Sudan ta Kudu kaura zuwa wasu tsofaffin barikokin soji da ke kan tudu.
Kauyen Canal da ke jihar Jonglei ya kasance wani wurin da sojoji suka taba amfani da shi a baya, shi da birnin Malakal da ke gaba da nan, dukkaninsu suna gefen Kogin Nilu.
Sai dai sabbin mazauna wurin sun fada cikin wani tashin hankali, bayan da suka fahimci cewa akwai wani tsohon inda da aka binne bama-bamai a wurin.
Mutanen da yaki ya kore su daga gidajensu sun shiga gujewa ambaliyan ruwa da ta kusan kai wa ga garin Bentui a jihar Unity.
Lamarin da ke ci gaba da zama wata babbar matsala a cikin shekara hudu da suka gabata.
An yi kiyasin cewa mutane miliyan 2.2 watau kusan kashi 20 cikin dari na al'umar sun rasa matsugunansu a cikin kasar.
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana fargabar cewa, kimanin mutanen kasar miliyan 10 za su bukaci tallafin abinci a shekarar 2023.
A wani yunkurin ganin ta tseratar da iyalinta daga ambaliyar da ta shanye kauyensu, Mary Nyantey (wadda ke cikin hoto na sama) ta daure 'ya'yanta biyar a wata ledar da ake amfani da ita wajen rufe gidaje saboda ruwan sama.
Inda ta shafe tsawon kwana guda tana iyo a cikin kogin, tana jan buhun da yaran ke ciki har ta isa garin Bentiu.
A yanzu iyalin na zaman gudun hijira a can, amma ba su da abinci sai suke zuwa kogin suna shuka wani abin da ake kira "yell", abin da suke ci kenan domin su rayu.
Sansanin 'yan gudun hijirar da ke Bentiu na dauke da mutane fiye da 112,000 kuma sansanin na sama wani tudun da aka gina don kare ambaliyan ruwa.
Jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Joshua Kanyara, ya ce wurin a bushe yake saboda ginin da kungiyoyin agaji suka yi ya kai tsawon mita 2.5 (kafa 8 da inci biyu).
Gatkuoth Makal Kuir (wanda ke hoto na sama) yana da shekara 19 lokacin da ya isa sansanin 'yan gudun hijirar a shekarar 2014, bayan ya kwashe kwana hudu yana tafiya da kafa, domin tserewa dakarun gwamnati da suka ce kauyensu na boye abokan gaba.
A yanzu shekarsa 27, kuma yana son komawa gida, amma baya jin zai iya daukar nauyin matarsa da dansa idan sun koma saboda ambaliya.
Yana wuni wajen neman itace, inda yakan yi tafiya mai nisan gaske, a don haka rashin tsaro na damunsa, musamman ma saboda rahotannin da suka samu na cewa dakaru sun kwashe wasu matasa 30, inda suka tilasta musu shiga soji kuma aka kashe su a fagen daga.
Nyawoura Dak Top (wadda ke hoto na sama) ta yi zaman gudun hijira a wani sansani da ke kasar Kenya,ta dawo wannan sansanin a bara domin neman mahaifiyarta.
An shaida mata cewa ta rasu a lokacin da aka fara yakin, amma lokacin da ta ji cewa mai yiwuwa tana Bentiu, sai ta zo nemanta.
Sun shiga cikin farin cikin da baya misaltuwa a lokacin da suka hadu, kuma tun daga sannan suke zaune tare.
Sai dai Nyawoura tana jinta a takure, a wannan sansanin saboda ci gaba da fuskantar ambaliyan ruwa. Tana so ta yi karatu, amma tana tsoron 'yan uwanta za su iya yi mata auren dole.
Yayin da mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa, a yankuna 36 cikin 79 na Sudan ta Kudu, ya sa mutane ba za su iya komawa aikin noma don samun kudin shiga ba da kiwon shanu, abin da ke da muhimmanci ga arziki da matsayin mutane a cikin al'umma, lamarin ya kuma shafi dabbobi yasa suna kanjamewa da mutuwa.
Yayin da mutane mutane da dama suka dogara da kayan agaji, wadanda a mafiya yawancin lokuta ta jirgen sama ake kaisu, mazauna sansanin na Bentiu sun shiga fargaba, ganin cewa kudaden agajin sun ragu zuwa kashi 67 cikin dari na abin da ake bukata.
"Masu bayar da agaji da su muka dogara, su ne iyayenmu, abincinmu, iliminmu, matsugunanmu da kuma samar da tsaronmu.
Idan babu su duka mutanen da ke wanna sansani mutuwa za su yi," a cewar wani dattijo dan gudun hijira mai shekara 80 a duniya, Diw Luong Peat (wanda ke hoto na sama).
A matsayinsa na wani babban sarki ya kasance yana da iyalai da matan aure da dama.
Sai dai tun shekarar 2014 aka kashe 'ya'yansa guda takwas a yakin, yayin da wasu 15 kuma cututtuka suka yi ajalinsu. Saboda batun rashin tsaro baya jin zai iya komawa gida.
Haka kuma yana da hatsari ga iyalai, kamar wadanda ke cikin hoton nan a Abyei, wani gari da ya yi makwabtaka da Sudan, su iya bacci kuma su rayu a gefen ruwan da ke kwance, a cewar kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières.
Ruwan da baya gudu ya taimaka wajen karuwar cutar malariya da wasu cututtukan da ake samu daga gurbataccen ruwa da matukar tamowa da karin sarar macizai da karuwar ciwon sukari.
Majalisar Dinkin Duniya ta sha nanata yiwuwar sake barkewar cutar kyanda.
Wani mazaunin Abyei, Dau Jach Chan, mai shekara 58, (na hotn sama) ya karbi bakuncin wasu iyalai biyu da suka rasa matsugunansu saboda ambaliyar ruwa, sannan ga rashin wajen zama ga masu gudun hijira a wani asibiti da bashi da nisa.
Yana kuma da 'ya'ya takwas don nhaka yana cikin fadi-tashin abin da zai sama musu dukkaninsu su ci.
Ga sabbin mazauna kauyen Canal kuwa (na cikin hoton sama), yanzu akwai fatan cewa za su iya yin shuka kadan.
A farkon wanna shekarar ne wata tawaga ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kwance bama-bamai (Unmas) suka kai musu dauki, inda suka gyara kasar da fadinta ya kai murabba'i 17,000 - inda suka gano fiye da bama-bamai 25 da aka binne.
Labarin hakan ya sa sun cika da murna kuma majalisar na fatan mutane kimanin 1,500 za su iya zama a wurin.
Sai dai Fran O'Grady jami'in Unmas ya jaddada cewa yanayin da ake ciki yana bukatar taka-tsantsa, ganin yadda mafiya yawan al'ummar Sudan ta Kudun sun samu kansu a gefen kogin Nilu, wurin da ya yi kaurin suna wajen fashi da tashin hankali tsakanin kasa da kasa.
"Abin bakin cikin shi ne mazauna kauyen da wadanda ke gudun hijira a kauyen Canal Village, basu da inda za su je, saboda dalilai na kabilanci da fadace-fadacen da aka yi a baya da kuma mallakar filaye," in ji shi.
"Idan da ace za su je neman matsugani a garin Malakal da ke can kasan kogin, za su jefa rayukansu cikin hatsari da saukarsu daga jirgin ruwa. "
Akwai hakkin mallaka na hotunan.
Christina Simons 'yar jarida ce mai zaman kanta da ke daukar hotuna don yin fina-finai kan abubuwan zahiri na kasa da kasa. Tana zaune ne a Iceland da ke Australia.