Dalilin da ya sa za a cefanar da hukumar sufurin jirgin ƙasa ta Najeriya

Ƙaramar Ministar Sufuri a Najeriya, Gbemisola Saraki, ta ce Gwamnatin Tarayya za ta raba hukumar kula da sufurin jirgin ƙasa ta kasar tare da sayar da ita ga 'yan kasuwa don inganta ayyukanta.

Misis Saraki ta yi magana ne a taron hadin gwiwa na kasa da kasa na Najeriya da aka gudanar a birnin Paris na Faransa.

Ta ce matakin zai haifar da gogaya a fanin sufuri jirgin kasa, tare da inganta kayayyakin more rayuwa da sauran kadarori.

Ta yi kira ga 'yan kasuwa na kasashen waje a wurin taron da su lalubo hanyoyin zuba jari a fannin, tana mai cewa matakin zai sake farfado da kimar kamfanin a cikin kasar da kasashen ketare.

"An sabunta alkawuran sufurin jiragen kasa a matsayin wani muhimmin bangare na sauyin zamantakewa da tattalin arziki," in ji ta.

"Abin lura shi ne daftarin tsare-tsare na shekara 25 da aka yi niyya don gyara duk wani layin dogo da ake da su, da gina sabbin layukan dogo tare da hada sauran tashoshin jiragen kasa."

Sai dai sanarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da ma'aikatan jiragen kasa su ka yi barazanar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3ranar Alhamis mai zuwa.

Ma'aikatan na neman a kara inganta tsarin albashinsu da jin dadinsu da kuma harkokin tsaro da suka shafi hanyoyin jiragen kasan.