An sanya dokar hana fita a wasu yankunan jihar Filato bayan kisan kusan mutum 30

Gwamnatin Jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce dokar hana fitar da ta saka ta zama ta zaman gida baki ɗaya biyo bayan kashe matafiya Musulmai da "matasan ƙabilar Irigwe" suka yi a Jos, babban birnin jihar.

Tun farko an ƙaƙaba dokar hana fitar ce daga 6:00 na yamma zuwa 60:00 na safe a ƙananan hukumomin Jos Ta Kudu da Jos ta Arewa da kuma Bassa. Amma ƙarin ya shafi Jos ta Arewa ne kaɗai.

A ranar Asabar ne matasan suka kashe matafiyan kusan mutum 30 sannan suka jikkata wasu kusan 50 a lokacin da suke wucewa ta cikin birnin zuwa Jihar Ondo bayan sun taso daga garin Bauchi.

Wata sanarwar 'yan sanda ta ce mutum 25 aka kashe yayin harin.

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya tura tawagar bincike ta musamman ƙarƙashin jagorancin DIG Sanusi N. Lemu.

Ya ƙara da cewa rundunar ta kama mutum 20 da ake zargin aikata kisan sannan ta ceto mutum 33 da aka raunata yayin harin.

An dauki matakin ne bayan wasu sun kashe aƙalla mutum 30 matafiya tare da jikkata wasu da dama a Jos babban birnin Jihar ranar Asabar.

Kwamishinan Watsa Labaran jihar, Dan Majang, ya faɗa wa BBC cewa sanya dokar hana fitar na da nasaba da kisan "matafiya musulmi 23 da ke kan hanyar su ta komawa kudancin Najeriyar daga jihar Bauchi."

Sai dai wasu bayanai na cewa adadin mamatan ya fi haka, kuma akwai da dama da suka tarwatse da har yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

A cewar Dan Manjang "matafiyan ƴan asalin jihar Ondo ne da suka fito daga jihar Bauchi bayan halartar wani taro sai wannan hargitsi ya rutsa da su."

Wasu rahotanni sun ce matafiyan sun halarci bikin sabuwar shekarar musulunci ne a garin Bauchi da ke maƙwabtaka da garin Jos na jihar Filato.

Kan ko sun san ko su waye su ka yi wannan ta'asa, Kwamishinan ya ce "ya yi wuri mu iya tantance ko su waye. Amma yanzu haka an kama kusan mutun 20 da ake zargi kuma yan sanda na kan yi musu tambayoyi."

Ya kuma tabbatar da mutuwar mutum 23 inda ya ce wasu ƙarin 23 suna kwance a asibiti.

Sai dai wani ɗan jarida da ya ziyarci asibitin yankin ya faɗa wa BBC cewa ya ga gawar mutum 30, yayin da wasu ke jinya.

Akasarin mutanen na ɗauke da sara na adduna da sauran makamai a jikinsu.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya haddasa rikicin, amma lamarin ya faru ne 'yan kwanaki bayan wani tashin hankali tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu manoma 'yan ƙabilar Iregwe.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, Gwamna Simon Bako Lalong ya yi tur da harin sannan ya gargaɗi "masu tayar da fitina da su guji yin hakan" saboda "gwamnati ba za ta lamunci tayar da hankali ba".

Da ma dai an shafe shekara da shekaru ana fama da rikicin kabilanci a jihar ta Filato, amma tun hawan Gwamna Lalong kan mulki lamuran tsaro sun inganta.