Me ya sa har yanzu aka kasa inganta ilimi a ƙasashe masu tasowa?

Shugabannin kasashe da wasu yankuna casa`in na halartar wani taro a birnin London da zai samar da tallafin ilimi ga kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.
Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson da shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ne suke jagorantar taron, wanda ake sa ran zai samar da dala biliyan biyar ga cibiyoyin da ke taimakawa wajen raya ilimi a duniya nan da shekaru biyar masu zuwa.
Sai dai wasu masana na zargin cewa ba kasafai irin wannan tallafin yake tasiri ba, sakamakon rashawa da son zuciya da suka dabaibaye shi.
Ana fatan za a yi amfani da kudin wajen inganta ilimin yara, musamman `ya`ya mata a kasashe masu tasowa a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Najeriya na cikin kasashen da ilimi, musamman a makarantun gwamnati ke fama da koma-baya sakamakon kalubale iri-iri, musamman ma matsalar tsaro, kasancewar `yan bindiga na kan kai hari kan makarantu, har ana sace dalibai domin karbar kudin fansa.
Irin wadannan hare-haren ne ma suka sa wata gamayyar kungiyoyin `yan kasuwa suka kaddamar da wata gidauniya mai suna Safe Schools Initiative da dala miliyon goma don samar da tsaro a wasu makarantu 500 a arewacin kasar.
Sai dai masana da ke bibiyar shirin na cewa har yanzu bai tsinanan wani abin a zo a gani ba.
Barrister Bulama Bukarti mai bincike kan harkar tsaro a nahiyar Afirka ya ce an bar jaki ne ana bugun taiki.
"Tsari ne da ke son ya kange makarantu daga sauran alumma ta hanyar kai karin jami'an tsaro da kuma amfani da na'urar zamani wanda abu ne da ba zai yiwu ba, tun da maharan idan su ka tashi kai hari, suna kai wa ne a daruruwansu," a cewarsa.
"Don haka idan za ka kai jami'an tsaro sai ka kai saman abinda su suke zuwa", in ji shi.
Barrister Bukarti ya ce ba mafita sai an dumfari matsalar daga tushe.
Su ma wasu masana a bangaren ilimi na ganin cewa raya ilimi sai da kudi, amma a Najeriya, suna zargin cewa irin wannan tallafi ba ya biyan bukata saboda matsalar rashawa da son zuciya daga masu ba da tallafin da masu karba.
Dokta Aliyu Tilde, wanda kwamishinan ilimi ne a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ya bayyana cewa sai an daina yin zobe ko bi-ta-da-kulli an kashe irin wannan kudi a kan ainihin matsalolin ilimi kafin a samu biyan bukata.
A ranar Juma'a ne ake sa ran kammala taron, kuma masana sun zuba ido su ga ko za a yi wani tsari daban da wanda aka saba gani, idan har kudin da ake sa ran tarawa ya samu.











