Wasu makarantun mata a jihar Kano babu kujerun zama

Wasu dalibai mata
Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ta ce miliyoyin 'yan mata ne ba sa samun zuwa makaranta saboda auren wuri da matsanancin talauci.

Wasu daga cikin dalibai mata a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, sun koka kan yadda suke fama da rashin kayan karatu kamar kujeru a azuzuwansu a makarantun da suke karatu.

Daliban na karatu ne wasu daga cikin makarantun sakandaren Mata da ke kananan hukumomin jihar, sun ce da dama daga cikin sun na fama da matsalar kayan zuwa makaranta sakamakon saurin tsufan da suke yi saboda zaman da suke yi a kasa.

A wata makaranta da wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya ziyarta a lokacin da suke karatu a karamar hukumar Gwaje, ya shaida cewa dukkan azuzuwan da ke makaranta babu kujera, yawanci su na zaune akan abin salla ko dan kwalinsu.

wata daliba ta shaida ma sa ''duka makarantar babu kujera, sai dai mu zauna a kasa ko sallayar gidnmu, sannan bai kamata a matsayinmu na mata mu dinga zama a kasa ba, sannnan mu na fama da matsalar Cinnaka, da kudin cizo su na damunmu a wajen zamanmu, mu na fada a gida amma babu yadda iyayenmu za su yi, mu na bukatar a taimaka ma na da kujeru.''

A wata makarantar ta daban da Khalifa ya sa ke ziyarta a karamar hukumar Nassarawa, ya gano dukka su na fuskantar matsala iri guda. Sai dai wani malamin makarantar ya ce sun shaidawa wadanda alhakin hakan ya shafa amma shiru.

''Gaskiya kam babu kujerun zaman dalibai, mun yi magana amma har yanzu ba a kawo ba, amma babu wani bayani da zai gamsar da kai cewa za a yi hakan, mun yi kokarin janyo iyayaen dalibai domin mu ga yadda za a magance matsalar, amma sun ki amimcewa saboda wai gwamnati ta ce musu ilimi kyauta ne, to ka ga yaya za mu yi da su,'' inji malamin.

Sai dai da ya tuntubi iyayen yara kan batun sun musanta, daya daga cikinsu ya ce da me iyaye za su ji da tsadar kayan abinci da matsin rayuwa, alhalin sun shaida musu ilimi kyauta ne.

Kwamishinan ilimi a jihar Kanon Honarabul Sanusi Sa'idu Kiru ya shaidawa BBC cewa daman sun san da matsalar karancin kujeru a makarantu, kuma tuni gwamnati ta dauki matakin rarrabawa su ga irin makarantun da ke fama da matsalar, don haka nan ba da jimawa ba rabon zai kai irin makarantun matan da BBC ta kai ziyara.

A baya-bayan nan wani rahoton Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya na UNICEF ya bayyana cewar yara mata miliyan dari da talatin da biyu ne ba su zuwa makaranta a fadin duniya, sakamakon talauci da auren wuri da sauransu.