Bello Matawalle: Gwamnan Zamfara ya koma APC, ya sasanta da Abdul'aziz Yari

Mohammed Bello Matawalle

Asalin hoton, Zamfara State Government

Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle ya sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa ta APC mai mulkin ƙasar.

Mai taimaka wa gwamnan na musamman kan yaɗa labarai Zailani Baffa ne ya tabbatar wa da BBC batun komen gwamnan, wanda ya yi a ranar Talata da yamma.

An ɗauki tsawon lokaci ana raɗe-raɗin cewa gwamnan zai koma jam'iyyar APC.

Ko a wata hira da BBC Hausa ta yi da Yariman Zamfara, Ahmad Sani a watan Yulin 2019, ya ce yana zawarcin Gwamna Matawallen kan ya bar PDP zuwa APC.

Gabanin komawar tasa dai, wasu jiga-jigan APC da suka haɗa da gwamnoni sun tare a gidan tsohon gwamnan jihar Abdul'aziz Yari domin neman goyon bayansa ga babban kamun da jam'iyyar za ta yi.

An ga hotunan shugaban jam'iyyar na APC da gwamnonin jam'iyyar tare da tsohon gwamnan na Zamfara.

Wani na kusa da tsohon gwamnan ya shaida wa BBC cewa an yi taron ne a Kaduna yayin da Gwamna Matawalle ke shirin tabbatar da shiga APC.

Daga cikin waɗanda suka halarci bikin sauya shekaƙar har da gwamnonin Kano da Kaduna da Kebbi da Borno da Kogi da Neja da Yobe da Ogun da Katsina da Jigawa da kuma Filato.

Sannan tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ma ya halarta.

Wannan layi ne

Daga yanzu Matawalle ne jagoran APC a Zamfara - Maimala Buni

Maimala
Bayanan hoto, "Za ku saurari sauran shirye-shirye na samar da sabuwar jam'iyya daga wajensa nan gaba kaɗan," in ji Buni.

Shugaban riƙo na jam'iyyar APC ta ƙasa kuma gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ya ce daga yau Gwamna Bello Matawalle ne jagoran jam'iyyar a jihar Zamfara.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar jim kaɗan bayan komawar Matawalle APC.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun mai taimaka wa gwamnan na musamman kan harkokin watsa labarai Zailani Baffa, ta ambato Mai Mala na cewa: "Daga yanzu Matawalle ne jagoran jam'iyyarmu mai girma a jihar Zamfara."

"Za ku saurari sauran shirye-shirye na samar da sabuwar jam'iyya daga wajensa nan gaba kaɗan," in ji Buni.

A lokacin da yake karɓar tutar jam'iyyar, Gwamna Matawalle ya karɓi jagorancinta a yayin da ya ayyana kansa a matsayin mamba a cikinta.

Kazalika Gwamna Matawalle ya shiga jam'iyyar ne tare da dukkan sanatocin jihar da ke kan mulki a yanzu, da ƴan majalisar wakilan tarayya shida daga cikin bakwai da kuma dukkan ƴan majalisar dokokin jihar.

Da yake magana a wajen taron sauya sheƙar, tsohon gwaman Zamfara Abdulazeez Yari, ya ayyana goyon bayansa da kuma jajircewa don samun nasarar jam'iyyar, tare da addu'ar neman tsarin Allah daga duk wata masifa da za ta sake samun jam'iyyar.

Wasu hotunan lokacin da gwamnonin APC suka je rarrashin Yari

Gidan Yari

Asalin hoton, Murtala Shehu City

Gidan Yari

Asalin hoton, Murtala Shehu City

Gidan Yari

Asalin hoton, Murtala Shehu City

Gidan Yari

Asalin hoton, Murtala Shehu City

Akwai kuma gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da sanata Modu Sheriff.

Rahotanni sun ce gwamnonin na ƙoƙarin shawo kan Abdul'aziz Yari domin ya amince da tafiya tare da gwamnan Zamfara Bello Matawalle.

Wannan layi ne

An yi ta ce-ce-ku-ce kan yunkurin komawar Matawalle jam'iyyar APC

Ana ci gaba da muhawara kan sauyin sheƙar da Gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle zai yi nan gaba zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

An shafe tsawon lokaci ana yaɗa jita-jitar cewa gwamnan yana shinshina jam'iyya mai mulki kafin APC ta tabbatar da komawarsa a ƙarshen mako.

Sai dai a iya cewa yayin da APC ta shirya gagarumar tarba kan wannan ƙaruwa da ta samu, sauyin sheƙar ga alama ya tayar da ƙura mai girman da ba san lokacin lafawar ta ba a nan gaba.

Rahotanni masu ƙarfi na cewa a ranar Talatan nan ne ake sa ran gwamnan zai sauya sheƙa daga jam'iyyar siyasa ta PDP zuwa ta APC.

Wannan layi ne

'Dole ya sauka daga gwamna'

Matawalle

Asalin hoton, Getty Images

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce da zarar Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa APC mai mulki to zai sauka daga mukamunsa.

Shugaban Jam'iyyar Uche Secondus ne ya bayyana haka ga manema labarai, cikin wani bidiyo da PDP ta wallafa a shafinta na Facebook.

Secondus ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, ya yi bayani a fayyace kan yadda za a iya warware wannan dambarwa.

Ya ce "kujerar da aka zaba, an zabi PDP ne ba wani mutum na daban ba, don haka in Matawalle ya bar wannan jam'iyya to za mu nemi dan jam'iyyarmu ya ci gaba da shugabancin Zamfara" in ji Secondus.

Sai dai wannan halayyar ta zama ruwan dare gama duniya a siyasar Najeriya, domin ita ma jam'iyyar ta PDP ta ci gajiyar sauya sheka a baya.

Misali, gwamnan Binuwai Samuel Ortom da na Edo Godwin Obaseki duka sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a cikin wa'adin wannan gwamnatin.

Sai dai yayin da jam'iyyarta PDP ke murza kambu, rahotanni daga Gusau, babban birnin na jihar Zamfara na cewa ana can ana ta shirin wani gagarumin bikin tarbar gwamna Muaawallen daga PDP zuwa APC.

Kuma ana sa ran gwamnan zai sauya sheka ne da magoya dubban bayansa, ko da yake akwai wadanda ba za su bi shi ba.

Cikin wadanda ba za bi gwamnan ba, akwai dan majalisar tarayya daga jihar, Kabiru Yahaya Classiq.

"Na zabi in tsaya ne a PDP bisa ga alkawarin da na dauka tsakanina da Allah. babu dalilin da Allah zai ba ni nasara a nan, sai in dauki ba zai ba ni wata nasara ba sai in na koma can."

Wannan layi ne