Rashin tsaro: Buhari ya bai wa ƴan bindigar Zamfara wa'adin wata biyu su miƙa wuya

Asalin hoton, Matawalle Twitter
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bai wa ƴan bindigar da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya wa'adin wata biyu su miƙa wuya.
Gwamnan jihar Bello Matawalle ne ya faɗi hakan a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata da daddare.
Gwamna Matawalle ya kuma ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin kai ƙarin dakarun tsaro 6,000 jihar don murƙushe ƴan bindigar idan har suka ƙi miƙa wuya.
Jawabin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ƴan fashi a ƙauyuka da kuma satar mutane ke ƙaruwa a jihar.
Gwamna Matwalle ya ce Shugaba Buhari ya yi wannan alƙawari ne a lokacin da ya kai wata ziyarar aiki Abuja don gana wa da shugaban da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ambato.
"A tattaunawar da na yi da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan masu ruwa da tsaki a Abuja, an yanke shawarar cewa za a kawo ƙarin dakarun tsaro 6,000 don su haɗa hannu da waɗanda ke ƙasa wajen daƙile matsalolin tsaron jihar.
"Nan ba da daɗewa ba dakarun za su iso jihar don fara ayyukansu, kuma muna godiya ga gwamnatin tarayya.
"Sannan kuma shugaban ƙasa ya amince da ƙayyade lokacin da ya kamata ƴan bindigar su miƙa makamansu su kuma shiga cikin shirin sasantawar da ake yi," a cewar gwamnan.
Sulhu ya gagara ne?
Ana ganin wa'adin da aka ba ƴan bindiga sauyin manufa ce ga ikirarin da gwamnatin Matawalle ta sha yi cewa gwamnatinsa tana sulhu da yan bindiga.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya sha fitowa yana ikirarin samun nasara a sulhun da yake yi da ƴan bindiga.
Ya taɓa fada wa BBC cewa sulhu ne kaɗai hanyar tabbatar da dawamammen zaman lafiya daga matsalar 'yan fashin daji da suka addabi yankin arewacin maso yammacin kasar.
Kuma har yanzu duk da wa'adin wata biyu da aka ba ƴan bindigar, gwamnatin Zamfara ta ce tsarinta na sulhu yana nan. "Ba wanda ya fi tsari mafi inganci kan ƴan fashi kamar gwamnatin Zamfara," in ji Zailani Bappa mai taimakawa gwamna Matawalle kan harakokin watsa labarai.
"Gwamnati za ta yi bakin kokari domin ganin an ci gaba da yin sulhu," in ji shi.
Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta riga ta yanke hukunci kuma komi gwamnatin tarayya ta yi ya danne na gwamnatin jiha.
Gwamna Matawalle tun bayan hawansa mulki ya ƙaddamar da shirin sasantawa da ƴan bindigar, abin da gwamnatin jihar take ganin yana aiki.
"Yarjejeniyar sasantawa da gwamnatina ta yi nasara wajen kuɓutar da ɗaruruwan mutanen da aka sace da buɗe kasuwanci da dawo da harkokin kasuwanci a faɗin jihar.
30,000Yawan ƴan bindiga
10,000Yawan dakarun tsaro da ke jihar
6,000Yawan dakarun tsaro da za a ƙara
Sai dai gwamnan ya ce duk da cewa an dan samu zaman lafiya sakamakon sasantawar, wasu ƴan bindigar har yanzu sun ƙi shiga cikin shirin suna ci gaba da kai hare-hare kan wasu al'ummomin.
"Kuma gwamnati ta gano masu yi mata ƙafar ungulu a ciki da wajen jihar kan harkar tsaro," in ji Matawalle.
Akwai ƴan bindiga 30,000 a jihar Zamfara
Jawabin gwamnan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da sarakunan gargajiya na jihar suka ce akwai fiye da ƴan bindiga 30,000 a fadin jihar Zamfara.
Sarakunan sun gaya wa hafsoshin tsaron ƙasar wannan magana ne a yayin da suka kai ziyarar aiki jihar.
Sun ƙara da cewa yawan ƴan bindigar ya fi na jami'an tsaro 10,000 da a yanzu haka ke jihar don yaƙi da masu kai hare-haren.
Gwamnan ya bai wa sarakunan gargajiyan da shugabannin ƙananan hukumomi umarnin sa ido kan shige da ficen duk wani da ba a gamsu da shi ba.
Kazalika ya haramta ɗaukar fiye da mutum biyu a kan babur. "Babu zirga-zirgar babura a duk lungu da saƙon jihar kuma an bai wa jami'an tsaro umarnin kama duk wanda ya karya doka," a cewarsa.
Sabbin matakan tsaro da gwamna ya sanar

Asalin hoton, Matawalle Twitter
- Za a bindige duk wanda aka gani da bindiga ƙirar AK47
- Sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomi su dinga zama a garuruwansu
- An haramta amfani da babura da yawa a lokaci ɗaya
- Za a hukunta duk wanda aka kama da yada labaran karya a kafafen sada zumunta
- Za a hukunta duk dan siyasar da aka kama da haddasa rikici da ɓata lamarin tsaro
- An hana mutum biyu hawa babur ɗaya
- Matawalle ya kuma jaddada haramta ayyukan ƴan sa kai a jihar, inda ya ce za a hukunta duk wanda aka kama da bindiga.












