ACF ta kalubalanci Matawalle ya fadi sunayen wadanda suka sace daliban Jangebe

Matawalle

Asalin hoton, Zamfara Govt

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattijan Arewa a Najeriya wato Arewa Consultative Forum ta yi kira ga gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya fito ya bayyana sunayen mutanen da ya yi iƙirarin cewa suna da hannu a satar ɗaliban Sakandiren Jangebe 279.

A ranar Talata ne aka sako ƴan matan bayan sun shafe kimanin kwana biyar a hannun ƴan fashin dajin da suka sace su tun ranar Juma'a.

Sau uku ke nan ana satar ɗumbin ɗalibai suna cikin makarantunsu a cikin ƙasa da wata uku a Najeriya.

Ƙungiyar ACF ta ce matuƙar Gwamna Bello Matawalle ya ƙi bayyana ko su wane ne ke da hannu a satar ɗaliban Jangebe, to kamata ya yi hukumomin tsaro su ɗauke shi a matsayin wanda ake haɗa baki da shi wajen satar mutane don neman fansa.

Murtala Aliyu, shi ne babban sakataren ƙungiyar kuma ya shaida wa BBC sun kaɗu sosai da yadda gwamnan na Zamfara ya fito ya bayyana cewa ya san waɗanda suke aikata wannan lamari.

"A matsayinsa na gwamna wanda haƙƙin jama'a ke kansa, ya zama yana da labarin waɗanda suke kawo matsaloli irin wannan, ya kamata a tuntuɓ shi a san su wane suke wannan kuma a ɗauki matakan dakile shi". in ji Murtala Aliyu.

Ga cikakkiyar hirar da Murtala Aliyu ya yi da BBC, kuna iya latsa alamar lasifikar da ke ƙasa domin saurara.

Bayanan sautiCikakkiyar hirar da babban sakataren ƙungiyar ACF ya yi da BBC