GGSS Jengebe: An sako 'yan matan makarantar sakandare a Zamfara

Yan matan Jangebe

Asalin hoton, Zamfara Govt

Gwamnatin jihar Zamfara a Najeriya ta tabbatar da sakin ƴan matan makarantar Jangebe da ƴan fashin daji suka sace.

Gwamnatin ta ce ƴan matan su 279 da aka sace sun shaƙi iskar ƴanci bayan ƙoƙarin da aka yi na ganin sun kuɓuta sannan dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ƴan fashin daji suka kutsa cikin makarantar tare da sace su.

Da sanyin safiyar Talatar nan BBC ta tattauna da gwamna Bello Matawalle na jihar ta Zamfara kuma ga ƙarin bayanin da ya yi:

"Alhamdu lillahi, mun ci nasara ga su an sako su dukansu. Dama guda 279 ne, kuma ga shi yanzu suna shigowa, yanzu muke karbar su da ni da mai dakina. Ga su suna shiga gidan gwamnati yanzu ga baki ɗaya."

Wane hali ƴan matan ke ciki?

Gwamna Matawalle: Ga su nan lafiyarsu lau. Kun ji maganganunsu, an kara muku su kun ji su suna magana.

"Saboda haka bukatar mu dama ita ce Allah ya dawo mana da su cikin koshin lafiya, kuma ga su nan sun dawo babu wani abu da ya same su, babu kuma wadda ta halaka cikinsu.

To ko an biya kuɗin fansa kafin aka sako su?

Gwamna Matawalle: Babu abin da aka biya. An yi komai ne bisa tattaunawar da muka yi da waɗanda su ka shiga tsakani aka yi sulhu.

"Yanzu su ma gasu nan su wajen talatin da wani abu da suka tafi suka tarar da wadanda su ka sace 'yan matan, sun yi maganganu da su kuma suka amso mana su.

Me Buhari ya ce?

A nasa ɓangaren Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin game da sakin daliban nan mata da aka sace a jihar Zamfara.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar , Buhari ya ce, "Zan shiga sahun iyalin da mutanen Zamfara na taya daliban da aka sace murnanr dawowa gida."

Shugaba Buhari ya kara da cewa ya yi murnar dawowar daliban gida ba tare da wata cutuwa ba, ya kara da cewa "tsare mutum ba karamin tashin hankali ba ne ba kawai ga wadanda aka kama ba, har ga iyalansu da kuma mu ba ki daya."

Buhari ya yi kira ga mutane da su zama masu sanya idanu kan yankunan da suke tare da bayar da cikakken hadin kai ga jami'an tsaro domin dakile hare-haren barayin dajin da wuri.Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna farin cikin game da sakin daliban nan mata da aka sace a jihar Zamfara.

An abandoned bunker bed in Kankara school
BBC
Satar ɗalibai a Najeriya

  • Ɗalibai 1,030 Aƙalla, aka yi garkuwa da su a makarantu a arewacin Najeriya tun 2014

  • Ƴan mata 276Boko Haram ta sace a Chibok a ranar 14 ga Afrilun 2014

  • Ƴan mata 110 Boko Haram ta sace a Dapchi a ranar 18 Fabrairun 2018

  • Maza 300Aƙalla ƴan bindiga suka sace a Kankara a ranar 11 ga Disamban 2020

  • Maza 27 Ƴan bindiga suka sace a Kagara a ranar 17 Fabrairun 2020

  • Ƴan mata 317Ƴan bindiga suka sace a Jangebe a ranar 26 ga Fabrairun 2020

Source: BBC

'Farin ciki ya lulluɓe mu ba a yi wa yaran fyaɗe ba'

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara Abubakar Dauran ya shaida wa BBC Pidgin cewa farin ciki ya lulluɓe gwamnati saboda ƴan bindigar ba su yi wa ko ɗaya daga cikinƴan matan nan fyaɗe ba a lokacin da suke tsare a hannunsu.

"Abin da muka fara yi bayan da muka karbi yaran shi ne tambayarsu ko wani abu ya same su da suke buƙatar kulawar gaggawa, cikin sa'a sai muka tabbatar da cewa ba su taɓa ko ɗaya daga cikinsu ba, sai farin ciki ya cika mana ciki."

Sai dai kwamishinan ya ce duk da haka sun gayyaci ma'aikatan lafiya da su zo su fara duba yaran nan ɗaya bayan ɗaya ba tare da ɓata lokaci ba a nan asibitin Gidan Gwamnati da ke Gusau.

Ta yaya harin ya faru?

Da misalin ƙarfe 1 na tsakar daren Alhamis ɗin da ta gabata ne ƴan bindiga suka kai hari makarantar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Zamfara Abubakar Dauran ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN cewa, ƴan bindigar za su kai 100.

Sace-sacen ɗalibai da aka yi a Najeriya kafin na Jangebe

Kagara (2021) - ɗalibai 27 da wasu mutum 15 ɗin

Kankara (2020) - 344 ɗalibai maza

Chibok (2014) - 276 ɗalibai mata

Dapchi (2018) - 113 mata

- An sako ɗalibai 344 na Kankara

- Har yanzu ba a ga ɗalibai 112 na ƴan matan Chibok ba

- An sako ɗalibai 107 na Dapchi. An kashe shida sannan har yanzu ba a ga Leah Sharibu ba

Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan batun dawowar yaran nan na Jangebe. Ku ci gaba da sabunta wannan shafin don ƙrin bayani.