Rashin yin yaren bebaye a gidajen talabijin da ke Najeriya na janyo wagegen giɓi – Masana

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Nijeriya ta ce nan ba da daɗewa ba za a fara ganin masu fassarar maganar kurame a tashoshin talbijin ɗin ƙasar don isar da labarai ga masu matsalolin ji.
Ministan labaran Nijeriya, Mista Lai Mohammed ne ya sanar da haka lokacin da yake ganawa da shugabannin Cibiyar 'yan ƙasa masu matsalolin nakasa yayin wata ziyara a Abuja.
Ya ce Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta ƙasar ta tabbatar da ganin tashoshin talbijin na aiki da wannan umarni a lokacin yaɗa labaransu.
Farfesa Jibrin Isah Ɗiso, malami a sashen koyar da masu buƙata ta musamman cikin Jami'ar Bayero Kano ya yi maraba da wannan matakin inda ya ce alama ce ta cewa gwamnati ta fara janyo masu buƙata ta musamman a jika.
Ya ce wannan gagarumin matakin a cewarsa zai sa "kuramenmu ko masu matsalar kunnuwa za su ji an jawo su a cikin gari kuma za su ba da mamaki wajen taimaka wa gwamnatin Najeriya".
Ya ce akwai wagegen giɓi da ake samu saboda rashin magana ta hannu a tashoshin talbijin saboda "mutanen nan suma suna jin kansu suma ƴan Najeriya ne, ya kamata a ce duk sauran abin da ake yi wa sauran masu kunnuwa masu idanu da sauransu, su ma ya zamana ana jansu, akwai manyan sakatarori a cikinsu, akwai waɗanda idan an ba su taimako, toh babu abin da masu matsalar kunnuwa ba za su iya yi ba,"
"Abin da kawai suke nema a ja su a jiki, ka da a nuna musu wariya a ce su ai ba sa ji". in ji Farfesa Ɗiso.
Da yake magana kan naƙasun da rashin sa maganar hannu a tashoshin talbijin ke da shi ga masu matsalolin ji, Farfesa Ɗiso ya ce akwai buƙatar a zauna a koyawa mutanen sunan ranaku, sunan watanni.
Ga cikakkiyar hirar da Mukhtari Admu Bawa ya yi da Farfesa Jibrin Isah Ɗiso:












