Ranar Bebaye Ta Duniya: 'Dalilan da ke sa wa a haifi bebaye'

Dr Halima 'Yar Fulani

Asalin hoton, Dr Halima 'Yar Fulani

Bayanan hoto, Dr Constanza ta nemi a rinka koyar da harshen bebaye a makarantu

Dr. Halima 'Yar Fulani wadda Bajamushiya ce da ke aiki a wata jami'a da ke kudancin kasar Jamus, ta ce akwai dalilan da ke sanyawa a haifi mutum da larurar bebantaka.

Dr Halima da ke nazari kan harshen Hausa ta ce, "akwai dalilai da yawa da ke sa mutum ya zama bebe ko a haife shi bebe musamman ma idan uwa ta sha wani magani lokacin da take da juna biyu. Sannan kuma cutar sankarau na daya daga cikin cututtukan da ke haifar da bebantaka."

Majalisar Dinkin Duniya da ta ware ranar 23 ga watan Satumbar kowacce shekara, domin nusar da al'umma da sauran masu ruwa da tsaki wajen fahimtar irin bukatar da ake da ita ta wajen fadada harshen bebaye domin su ma a tafi tare da su.

Hakan ne ya sa Dr Halima ta ce "wannan rana ta harshen bebaye na da muhimmanci sosai saboda dalilai guda biyu: tana sanar da mu cewa harshen bebaye harshe ne na ainahi wato kamar sauran harshen duniya yake misali kamar Larabci ko Turanci ko Hausa.

Sannan kuma ranar tana tunatar da mu irin hakkin bebaye ke da shi na yin amfani da harshensu."

Halima 'yar Fulani ta kuma bayyana bukatar da ake da ita ga likitoci da lauyoyi da sauran kwararru wajen fahimtar harshen bebaye domin samun damar tattaunawa da su lokacin da bukatar hakan ta taso.

To sai dai masaniyar harshen na bebaye ta kara da cewa "amma abin da ya fi shi ne a koyar da harshen bebaye a jami'a da kuma tafinta domin samun mutanen da za su iya yin aikin tafinta a duk wuraren da ake bukatar su ko a asibiti ko a kotu koma a jami'a."

Hakan a cewar Dr Halima "zai bai wa bebaye damar yin karatu har zuwa matakin digiri domin zama likita ko lauya da sauransu."

Short presentational grey line

Ko me ya sa bebaye ba sa son hulda da sauran jama'a?

Halima Costanza
BBC
Akwai dalilai da yawa da ke sa mutum ya zama bebe ko a haife shi bebe, musamman ma idan uwa ta sha wani magani a lokacin da take da juna biyu."
Dr Contanza Halima Shamailing
Malama a wata jami'a da ke kudancin kasar Jamus

Mafi yawancin lokaci, bebaye kan kasance tare da junansu domin tattaunawa, inda a wasu lokutan ma a kan samu yanayin da bebaye kan bar gidajensu domin zuwa wurin 'yan uwansu bebaye.

Dr Halima ta ce "ka taba zuwa kasar da ba ka jin yarensu? To su bebaye haka suke saboda haka ai babu mamaki domin bebe ya tafi wurin sauran bebaye domin su tattauna.

Amma akwai mutanen da ke jin harshen na bebaye musamman a ƙauyuka inda suke tattaunawa cikin harshensu wato maganar hannu.

Kuma sun koyi wannan yaren ne saboda ko dai suna da 'yan uwa bebaye ko maƙwabta ko kuma saboda suna sha'awar harshen bebaye."

'Ayyukan da na yi kan harshen bebaye'

Dr Halima 'Yar Fulani ta ce ta yi ayyuka da dama da manufar inganta harshen bebaye "mun riga mun yi litattafai guda takwas a fannoni daban-daban misali kasuwanci da lokaci."

Yanzu dai malama Halima ta ce tana kan aikin littafi na 9 a fannin addini sannan kuma ta ce "ana iya samun dukkannin alamomi da rubutun bebaye a manhajar maganar hannu."

Dr Halima 'Yar Fulani

Asalin hoton, Dr Halima 'Yar Fulani

Bayanan hoto, Dr Halima 'Yar Fulani ta ce bebaye sun fi yi hulda da mutanen da suka iya magana da harshensu
Wannan layi ne