Isra'ila: Ana shirin gina gidajen Yahudawa 8000 a matsugunan Falasɗinawa da aka ƙwace

Gaɓar yammacin kogin Jordan

Mahukuntan Isra'ila sun amince da gina ƙarin wasu gidaje kusan dubu takwas ga yahudawa 'yan kaka gida a gaɓar yammacin kogin Jordan da ta mamaye.

Wata ƙungiya mai da'awar neman zaman lafiya a Isra'ila, mai suna Peace Now, ta soki matakin da ta kira cin zali, sannan zai ƙara kawo tsaiko ga fatan sasanta rikicin dake tsakanin ƙsar da kuma Falatsdinawa.

Za a gina sabbin gidajen a yankin da Falasdinawa ke fatan wata rana zai dawo ƙarƙashinsu bayan ƙwace shi a baya.

A watan Nuwamba Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da abin da Isra'ila ta yi, wanda ta ce shi ne rusau mafi girma da aka yi wa gidajen Falasɗinawa a gabar yammacin kogin Jordan cikin sama da shekara 10.

Rusau ɗin ya raba mutum 73 da muhallansu ciki har da yara 41, bayan rushe inda suke zaune a Beduuin da ke Khirbet Humsa a tsaunukan Jordan, kamar yadda MDD ta ce.

Dakarun Isra'ila sun ce an yi gine-ginen yankin ne ba bisa ƙa'ida ba.

Sai dai MDD ta kira wannan mataki na Isra'ila a matsayin "sanya ƙafa a shure" dokar ƙasa da ƙasa.

Kamar yadda ofishin ba da agaji na MDD Ocha ya bayyana, gine-gine 76 ciki har da gidaje da burtalai da banɗaki da farantan samar da wuta mai amfani da hasken rana - duka aka rushe a yammacin ranar Talata.

Hukumomin Isra'ila sun ce adadin gine-ginen ba su kai haka ba, suna cewa "an gabatar da dokar ne" kan wasu tantuna bakwai da burtalan dabbobi takwas.

Wani bidiyo da hukumar kare hakkin ɗan adam ta Isra'ila ta fitar kan rushe gine-ginen, ya nuna yadda aka yi watsi da kayayyaki kamar gadaje da abin shimfida da kuma sauran kayayyakin gida.