Firaiministan Eswatini ya mutu bayan fama da Korona

Dlamini mai shekaru 52 ya mutu ranar Lahadi a wani asibiti da ke Afrika ta Kudu.
Bayanan hoto, Marigayi Ambrose Dlamini, firaiministan Eswatini

Gwamnatin Eswatini ta sanar da mutuwar Firaiminista Ambrose Dlamini, mako hudu bayan kamuwa da cutar korona.

Sanarwar gwamnatin ta ce Dlamini mai shekaru 52 ya mutu ranar Lahadi a wani asibiti da ke Afrika ta Kudu.

To amma sanarwar ba ta fito fili ta bayyana me ya yi ajalin Firanministan ba, amma Mr Dlamini ya shafe makonni hudu ya na jinyar cutar Covid-19.

Tun a watan Oktoban 2018 Ambrose Dlamini ya karbi ragamar jagorantar Eswatini, wadda aka fi sani da Swaziland.

Eswatini mai yawan al'umma da ba su wuce miliyan daya ba na da masu dauke da cutar korona 6,768 da mace-mace 127 kamar yadda alkaluman ma'aikatar lafiyar kasar suka nuna.

A ranar 16 ga watan Nuwamba ne Ambrose Dlamini ya sanar da cewa ya kamu da cutar ta korona amma ba mai tsanani ba.

To amma mako daya bayan haka a ranar 1 ga watan Disamba gwamnatin Eswatini ta sanar da cewa an garzaya da firaiministan wani asibiti a Afrika ta Kudu don duba lafiyarsa.

Daga nan gwamnatin ba ta sake fitar da wani bayani ba sai a wannan karon da ta sanar da mutuwarsa a ranar Lahadi.

Haka ma sanarwar wadda ke dauke da sa hannun mataimakin firanminista Themba Masuku, ta ce 'gwamnati tare da hadin gwuiwar iyalan Firaiminista Ambrose Dlamini za ta cigaba da sanar da yan kasa halin da ake ciki'.

Ambrose Dlamini wanda tsohon ma'aikacin banki ne ya sanar da sauya sunan kasar daga Swaziland zuwa Eswatini a shekarar 2018.