Rashin tsaro: Abubuwan da majalisa ke son sani daga Shugaba Buhari

Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari zaurenta domin ya yi mata bayani kan matsalar tsaron da ta addabi ƙasar.

Ƴan majalisar sun yanke shawarar gayyatar Shugaba Buhari ne bayan kisan da aka yi wa wasu manoma fiye da 43 a kauyen Zabarmari na jihar Borno.

Majalisar ta ce akwai buƙatar shugaban ya yi bayani a kan abin da ya hana karya-lagon mayaƙan Boko Haram duk kuwa da irin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a kan jami'an tsaro.

Honourable Satomi Ahmed, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin, ya shaida wa BBC cewa an ɗau wannan mataki ne ganin cewa an sha kiraye-kiraye ga shugaban kan neman sake fasalin harkokin tsaro amma babu shiru ake ji.

Bayanan da majalisa ke son samu daga Shugaba Buhari

Satomi ya ce yanayin da ake ciki ya tabbatar da cewa dole ana neman gyara, amma a iya sanin majalisa ta rasa dalilan shugaban ƙasa don haka ta buƙaci ya bayyana a gabanta.

Majalisar ta ce dole shugaban ya fito ya yi bayani mai gamsarwa kan irin matakan da yake ɗauka da kuma dalilan gamsuwa da ayyukan hafsoshin tsaron ƙasar da ake gani ya kamata a sake zubin su.

Sannan akwai kuma buƙatar sanin ina shugaban ya dosa, domin kashe-kashe da sace-sacen da ake gani ya wuce tunani.

Majalisar ta ce talakawa sun bai wa Shugaba Buhari amana don haka ba za su amince su ci gaba da zaman ƴan amashin shata ba, in ji Satomi.

Satomi ya ce ana su ɓangaren akwai gazawa a salon yaƙin da jami'an tsaron ke yi da matsalolin tsaro don haka za su so ji daga baƙin shugaban don sani halin da ake ciki.

Yaushe majalisar ke saran Buharin ya bayyana gabanta?

Majalisar dai ba ta bayyana ranar ko taƙamaiman lokacin da take saran Shugaba Buhari ya hallara a gabanta ba.

Sai dai a cewar Hon Satomi, nan ba da jimawa ba za a samu wannan bayanin domin dole su tashi tsaye lura da cewa tura ta kai bango.

Karin Labaran da zaku so karantawa

Sharhi

Yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu na sake ɗaga hankula da haifar da fargaba a kullum.

Tun sake rincaɓewar matsalolin tsaron ake ta kira ga shugaba Buhari ya sake fasali da sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

Amma da alama hakan ba lallai mai yiwuwa ba ne, don shugaba ya nuna alamomin yana gamsuwa da ayyukansu.

Ƴan ƙasa da dama na ganin lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya sauke nauyi da alkawaran da ya dauka na kare rayuka da dukiyoyi.

Fargabar zuwa gona na sake karuwa tsakanin manoma, haka zalika harkokin kasuwanci na baya saboda rashin ƙyan hanya da tsoron masu satar mutane.

Masana harkokin tsaro na cewa idan ba ayi wa tufkar hanci tun da wuri ba, to ana iya wayar gari cikin gagarumar matsala da koma baya a fannin tattalin arziki da ƙarancin abinci.