Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin Zabarmari: 'Mutum biyar aka kashe a gonata, biyu daga ciki 'ya'yana ne'
Wani magidanci a yankin Zabarmari da ke jihar Borno ta Najeriya, Malam Musa, ya shaida wa BBC cewa "mutum biyar aka kashe a gonata biyu daga ciki 'ya'yana ne" a harin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 43.
Lamarin, wanda ya faru ne a karshen mako, ya tayar da hankulan 'yan Najeriya inda wasu suka rika kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki suna masu cewa ya gaza kare rayukan al'ummar kasar.
Ɗansa, Musfau mai shekara 18, na cikin waɗanda aka kashe a harin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai shi a ranar Asabar, a ƙauyen Koshebe.
"Cikin yarana 16 Musfau na musamman ne saboda kwazon da yake da shi, yana taimaka mana sosai, mahaifiyarsa ta yi kuka sosai saboda abin da ya faru.
"Mun yi masa fatan a dawo lafiya kan ya tafi inda ya ke yi wa mutane aikin shin kafa su kuma su biya shi, ban san cewa ganina da shi na ƙarshe ba kenan, in ji shi.
"Da na kalli inda yake kwana da sauran kayayyakinsa sai in ji bakin ciki amma ba yadda za mu iya, Allah ya rubuta ƙaddararsa a haka."
Malam Musa ya ce ɗan nasa ya kammala SS2 a makarantar sakandire yanzu kuma yana daf da shiga shekararsa ta ƙarshe, yaro ne mai son neman na kansa bayan karatunsa.
A cewarsa: "Ko wacce shekara yana zuwa aikin gona dag ɗan kuɗin da yake samu ne yake taimakawa mutan gidan da mahaifiyarsa dama shi ne ɗanta na farko."
" A 'yan shekarun bayan nan, ko da yaushe mutane suka je gona to sai dai fa su dawo a guje, amma a wannan shekarar mafi yawan masu wannan gudu duk sun mutu ciki kuma har da ɗana." in ji shi.
Labbo Tanimu shi kuma 'ya'yansa biyu aka kashe da ma'aita uku a gonarsa, ciki har da wani Usman da ake shirin aurensa na ba da jimawa ba.
"Mutum biyar suka kashe a gonata ciki har da yara ba biyu, Musa da Usman, Shi Musa na da aure Usman kuma na shirin yi a kusa."
"A gonar muke samun abin da za mu ci ko yaushe, amma yanzu ba za mu iya zuwa ba saboda tsoro, gwamnati ta taimaka mana ta kawo karshen wannan bala'i."