Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a hanyar Zaria-Kaduna
Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na cewa an shafe daren Lahadi, wayewar garin Litinin ana musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Zaria zuwa Kaduna kusa da garin Jaji.
Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin a wata tattaunawa inda ya ce lamarin ya faru ne a kusa da garin Jaji.
Ya ce tun da suka samu labarin cewa 'yan bindigar sun kai harin, nan take aka aika da jami'an tsaro domin daƙile harin.
Wani mazaunin yankin ya ce a daren, ɓarayin sun tare hanyar da ke tsakanin Dumbi-Dutse zuwa Lamban Zango, haka kuma suka tare hanya tsakanin Jaji da Kwanar Faraƙwai.
Duk da cewa babu wasu cikakkun bayanai kan wannan harin daga kwamishinan tsaron, amma wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun kashe mutum biyu da ke cikin wata babbar mota ƙirar Luxirious, haka kuma jami'an tsaron sun kashe 'yan bindigar har mutum biyu.
Haka kuma ɓarayin sun raunata mutane da dama tare da garkuwa da su, sai dai wasu majiyoyi sun ce jami'an tsaro sun samu nasarar ƙwato wasu daga cikin waɗanda aka sace.
Ko a makonnin da suka gabata sai da 'yan bindigan suka kashe aƙalla mutum 16 a wasu yankuna na jihar da suka haɗa Zangon Kataf da Igabi da kuma Giwa.
Haka kuma 'yan bindigar sun sace wasu malamai da ƙananan yara daga cikin Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya, a wani lamari na daban kuma, sun ratsa Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria inda suka sace wani malami.
A makon da ya gabata kuma 'yan bindigar sun kashe mutum huɗu a hanyar Kaduna zuwa Abuja kusa da garin Kakau da ke daf da shiga ƙwaryar garin Kaduna.