Belgium ta kori wasu ƴan Denmark da ke shirin ƙona Alƙur'ani

Belgium ta iza ƙeyar wasu ƴan Denmark biyar masu ra'ayin riƙau sannan ta haramta musu shiga ƙasar har tsawon shekara guda saboda shirinsu na ƙona Alkur'ani a wani yanki da Musulmai suka fi yawa a birnin Brussels.

Sakataren kula da masu neman mafaka Sammy Mahdi ya bayyana su a matsayin "wata gagarumar barazana ga zaman lafiyar jama'a".

Kamar yadda shafinsu na Facebook ya nuna, mutanen biyar 'abokan wani ɗan siyasa ne mai tsattsauran ra'ayi Rasmus Paludan.

An kori Paludan daga Faransa ranar Laraba bayan nuna aniyarsa ta ƙona Alkur'ani a birnin Paris.

Tun da farko a bana, an ɗaure shi tsawon wata guda a Denmark saboda jerin wasu laifuffuka, ciki har da wallafa bidiyoyi na ƙin musulunci a shafukan sada zumunta na jam'iyyarsa Stram Kurs (mai ra'ayin riƙau).

A lamarin na baya-bayannan, ƴan sandan Belgium na zargin mutanen da shirin ƙona Alkur'ani a gundumar Molenbeek-Saint-Jean da ke birnin Brusseles, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka rawaito.

Akwai ƴan Maroco da dama a yankin.

Ƴan sanda sun yi musu tambayoyi wadanda kuma suka mika batun na su zuwa ofishin mai shigar da ƙara, kamar yadda wata majiya ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP ya rawaito

Shi ma Mr Mahdi, wanda ɗa ne ga wani ɗan Iraqi ɗan ci rani, ya yi maraba da kama su da kuma korarsu.

"An umarce su da su fice daga ƙasar cikin gaggawa, kuma sun fita ɗin, kamar yadda ofishinsa ya rawaito. "An ƙi amince wa da su ci gaba da zama saboda wadannan mutanen wata barazana ce ga zaman lafiyar a Belgium."

Sanarwar ba ta ambaci sunan Paludan ba amma ta ce "an kama wani mutum kwanannan a Faransa saboda irin wannan laifin".

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar 30 ga watan Oktoba, Paludan ya ce ya shaida wa ofishin jakadancin Faransa a birnin Copenhagen cewa zai ƙona Alkur'ani a Arc de Triomphe a birnin Paris ranar 11 ga watan Nuwamba.

Malam Mahdi ya ƙara da cewa: "A al'ummarmu da dama a rarrabe take, ba ma buƙatar mutanen da za su zo su yaɗa ƙiyayya."

A watan Agusta, magoya bayan Paludan a kudancin birnin Malmö na Sweden sun ƙona Alkur'ani, abin da ya janyo mummunar arangama da ƴan sanda.