Fashewar Beirut : An jiyo motsin rai a gurin da fashewar ta auku

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyoyin masu aikin ceto da ke neman wadanda mummunar fashewar nan ta Beirut ta ritsa da su cikin watan jiya a Lebanon, sun jiyo alamun motsin rai a baraguzan wani gini da ya rufta.
Masu aikin ceto daga kasar Chile sun ce sun jiyo motsin ne a wani yanki da ake kira Gemayzah.
Daya daga cikinsu ya ce na'urarsa ta jiyo karar bugun jini daga wani wuri cikin baraguzan mai nisan mita biyu.
Sun ce ana bukatar manyan injin daga nauyi don isa wurin.
Kimanin mutane dari da casa'in ne suka mutu a fashewar da sinadarin Ammonium Nitrate ya haifar.
Lebanon na cikin yanayi na matsalar tattalin arziki irin sa mafi muni tun yaki basasar kasar tsakanin 1975-1990, akwai matsalar wutar lantarki, babu ruwan sha mai tsafta ga kuma lalacewar asibitoci.
Darajar kudin kasar ya karye, kuma kasar ta kasa biyan basukan da ake bin ta wadanda wa'adinsu ya cika tun a watan Maris.
Tattaunawa da asusun lamuni na IMF kan karbar bashin dala biliyan 10 ya tsaya cak.
Akwai fargabar cewa iftila'in fashewar da aka samu a kasar ya sake kassara kokarin farfado da tattalin arzikinta.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da dala miliyan 100 ake bukata domin ayyukan gaggawa, kamar samar da abinci da ruwan sha, da kuma gine-gine da samar da asibitoci da makarantu.











