Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Neymar: Barcelona ta soma fitar da rai a kan dan kwallon Brazil
Zai yi wuya Barcelona ta iya sayen Neymar daga Paris St-Germain saboda yanayin da ake ciki na tattalin arziki, in ji shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu.
Akwai kuma alamun cewa dan kwallon Inter Milan Lautaro Martinez shi ma ba zai koma Barca ba.
Bartomeu ya shaidawa jaridar Spaniya cewa Barca ta samu kudin shiga kasa da Euro miliyan 200 daga watan Maris zuwa Yuni saboda annobar coronavirus.
"Lamarin ya yi matukar shafar manyan kungiyoyi a Turai," in ji shugaban kulob din.
"Tasirin zai wuce shekara guda, zai kai shekaru uku zuwa hudu".
Dan kwallon Brazil Neymar ya koma PSG a kan Euro miliyan 222 a watan Agustan 2017 amma sai Barcelona ta yi kokarin sake sayensa a kakar wasan data wuce.
"Neymar?A wannan yanayin, abin da kamar wuya," in ji Bartomeu
"Kuma PSG bata son ta siyar da shi".
"Barca mun soma magana da Inter a kan Lautaro, amma mun daina magana. Yanayin ya shafi harkar zuba jari."
Bartomeu ya kuma yi bayanin cewa Barcelona ta yi asara euro miliyan 200 saboda korona.