Ko Barcelona za ta iya cin Espanyol kuwa?

Barcelona za ta karbi bakuncin Espanyol a wasan mako na 35 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a Nou Camp ranar Laraba.

A wasan farko da suka buga a kakar bana a gidan Espanyol ranar 4 ga watan Janairun 2020 tashi suka yi 2-2.

Barcelona ta ci kwallayenta ta hannun Luis Suarez da kuma Arturo Vidal, yayin da David Lopez da kuma Wu Lei na Espanyol suka zura kwallo a ragar Barca.

Tun a sanyin safiyar Talata, Barcelona ta yi atisayen karbar bakuncin Espanyol, sannan ta bayyana wadanda za su buga mata karawar.

Kuma dukkan 'yan kwallon Barca sun halarci atisayen har da Frenkie de Jong, yayin da Junior ya motsa jiki shi kadai ba cikin 'yan wasa ba.

Dan wasan mai tsaron baya na fama da ciwon kugu, kuma ba zai buga karawa da Espanyol ba, za kuma ta auna koshin lafiyarsa nan gaba.

A ranar Lahadi Barcelona ta je ta doke Villareal 4-1, hakan ne ya bai wa kungiyar rage tazarar maki tsakaninta da Real Madrid ya koma hudu kawo yanzu.

Kocin Barcelona ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fafata da Espanyol. bai yi canji ba daga wadanda suka doke Villareal a ranar Lahadi ba.

'Yan kwallon Barcelona da za su fuskanci Espanyol:

Ter Stegen da N. Semedo da Piqué da I. Rakitic da Sergio da Arthur da Suárez da Messi da Neto da Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da Braithwaite da kuma S. Roberto.

Sauran 'yan wasan sun hada da, Vidal da Iñaki Peña da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da R. Araujo da Morer da Monchu i J da kuma Cuenca.

Wadanda ke jinya sun hada Queden da Dembélé da De Jong da Umtiti da kuma Junior.