Real Madrid na zawarcin Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na son dauko dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 26. (Sport)
Dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ba zai koma Manchester United da bazara ba idan basu samu gurbin buga Gasar Zakarun Turai ba. (Sun)
Leicester, Newcastle, Crystal Palace da kuma Aston Villa na sha'awar sayen dan wasan Rangers da Colombia Alfredo Morelos, mai shekara 23. (Talksport)
West Ham tana tattaunawa da jami'in Alexis Sanchez a yayin da suke duba yiwuwar dauko dan wasan gaban na Chile. Sanchez mai shekara 31 yana can Inter Milan a matsayin aro daga Manchester United. (Sport Witness)
Mai yiwuwa a bar dan wasan Manchester City dan kasar Spain David Silva, mai shekara 34, ya buga wasan bankwana a Etihad Stadium a bazara idan annobar coronavirus ta hana shi yin bankwana da masu goyon bayan kungiyar bayan ya kwashe shekara 10 yana buga tamaula a City inda ya lashe Kofin Firimiya sau hudu. (Mail)
Tsohon dan wasan Manchester United da Tottenham Dimitar Berbatov ya yi amannar cewa zai fi kyau idan dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 24, ya koma Bayern Munich maimakon Liverpool a bazara. (Mirror)
Leicester, Tottenham da kuma Everton dukkansu suna son dauko dan wasan baya mai shekara 25, Baptiste Santamaria, wanda ke murza leda a kungiyar da ke buga gasar League 1 a Faransa Angers. (Express)
Kungiyoyin da ke buga Gasar Firimiya sun sayi na'urorin yin gwajin kwayar cutar coronavirus na kashin kansu a yayin da ake fargaba game da buga wasannin bayan-fage. (Star)
Dan wasan Manchester United dan kasar Timothy Fosu-Mensah, mai shekara 22, yana fuskantar rashin makoma a yayin da kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer yake nazari kan ko ya kara masa kwangilar shekara daya. (Mirror)
Dan kasar Russia da ke murza leda a Celta Vigo Fedor Smolov, mai shekara 30, ya keta dokar hana fita a Spain ya koma kasarsa, inda ya kasance dan wasan kungiyar na biyu da ya karya dokar ta hana fita domin dakile yaduwar coronavirus. (AS, in Spanish)











