An sanya dokar ta baci kan farin dango a Somalia

An kaddamar da dokar ta baci kan zugar farin dango da suka addabi kasar Somalia da wasu kasashen gabashin Afirka.

Ma'aikatar noma ta kasar ta ce farin dake cinye shuke-shuke babbar barazana ce ga halin da Somalia ke ciki na karancin abinci.

Akwai kuma fargabar ba za a iya shawo kan matsalar ba kafin faduwar damina da ke zuwa a wata Afrilu.

Kasashe makwabta irinsu Kenya sun shafe shekara 70 ba su fuskanci barazanar fari dango irin na bana ba, inji hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO.

Somalia ce kasa ta farko a yankin da ta ayyana dokar ta baci domin yakar farin.

Matsalar rashin tsaro a kasar ya sa ba za a iya amfani da jiragen sama wajen yin feshi domin kashe farin ba.

A watan Janairu ne FAO ta bukaci kasashen su agaza a kawar da farin, tana mai cewa suna iya karuwa da kashi 500 a watan Yuni idan ba a dauki mataki ba.

Farin da suka yadu a yankin gabashin Afirka, sun taso ne daga Yemen sakamakon ruwan sama mai karfi a karshe-karshen 2019, abin da ya haifar da karuwarsu.

Kwarin kan yi tafiyar kilomita 150 a kullum kuma kowane babba daga cikinsu na kan ci adadin abincin da ya kai nauyinsa a rana.

A watan Disamba, wata zugar fari ta sa wani jirgin sama kauce hanya a kasar Itiyopia, bayan sun yi ta karo suna shiga injin jirgin da gilashinsa.

Amma jirgin ya sauka ba tare da wata asara ba a wani filin jirgi da ki birinin Addis Ababa.