Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An rufe wani babban kanti a Abuja saboda Coronavirus
Rahotanni daga Abuja, babban birnin Najeriya na cewa gwamnati ta rufe wani babban kanti a unguwar Jabi bisa zargin shigo da dabbobi da nama dangin ruwa ba bisa ka'ida ba daga China - kasar da aka samu barkewar cutar Coronavirus mai yaduwa.
Hukumar kare hakkin masu sayayya FCCPC a kasar ce ta dauki matakin rufe kantin ranar Laraba kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ta ce ta dauki matakin ne bayan wani samame sakamakon samun bayanai cewa kantin ya rufe saboda gudun abin da ka je ya zo game da cutar Coronavirus.
A cewar hukumar "an gano wasu kayayyaki da wa'adinsu ya cika jibge a kantin na Panda da ke Jabi a Abuja."
"Har da kayayyakin da wa'adinsu ke cewa shekarar 2089 da 2037 da 2018 da kuma 2019." in ji hukumar.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike domin kwashe duk wasu kaya da ke da barazana ga lafiyar jama'a.
FCCPC ta kuma ce ta samu bayanai da aka tabbatar cewa kantin ya killace wani waje na musamman domin al'ummar yankin Asia.
Rahotanni na cewa kantin ya shahara ne wajen sayar da barasa da kayayyakin jarirai da lemuka da kuma nama dangin ruwa.