Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Sama da mutane 100 sun mutu 4,515 sun kamu
Hukumomi a Chana sun sanar da cewa wadanda Coronavirus ta kashe sun haura mutane 100
Hakama sun sanar da cewa adadin wadanda suka kamu ya ninka.
Kididdiga ta nuna cewa kawo yanzu wadanda suka mutu sanadin cutar Coronavirus sun kai 106, kuma adadin wadanda suka kamu ya kai 4,515 daga 2, 800 a ranar litinin.
Wannan ne ya tada hankalin Sin, kuma a yanzu kasar ta kara tsaurara matakan hana zirga zirga da nufin hana yaduwar cutar.
Birnin Wuhan wanda nan ne Coronavirus ta fara bulla ya kasance babu shiga babu fita.
Babban abun da ya fi daga hankalin hukumomi shine rashin samun maganin wannan cuta da ke kawo matsala wurin numfashi.
Bincike ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka mutu tsofaffi ne ko kuma wadanda dama ke fama da wata cuta da ke da alaka da numfashin.
Kusan za a ce Chana ta rasa abunyi a yanzu, wurin ganin ta kawar da cutar.
Kuma masana na ganin yawan jama'a a yankin na daya daga cikin abubuwan da suka dada dagula al'amura.
Birnin Wuhan kawai na da mutun miliyan 11, baya ga sauran birane da ke yankin Hubei.
Ganin halin da a ke ciki ya sa kasashe a fadin duniya sun fara kira ga al'ummarsu da su kauracewa zuwa Chana.
Kuma tuni kasashe kamar Amurka ta fara shirin kwashe yan kasarta da ke Wuhan da ma ma'aikatan da ke ofishin jekadancinta a fadin kasar har sai yadda hali yayi.
A yanzu hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar da cewa mutane 47 sun kamu a wajen Chana, kuma Jamus ce ta baya bayan nan.
Kuma akwai hasashen cewa Coronavirus na shirin kutsa kai nahiyar Afrika.