Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kokarin sasanta Ganduje da Sarkin Kano —Ibrahim Shekarau
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Shekarau:
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce yana aiki ta karkashin kasa domin ganin an samu masalaha tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Yayin wata ziyara da ya kai ofishinmu na Landan, sanatan wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya ce a matsayinsa na daya daga cikin 'yan majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin Kano ba abu ne mai yiwuwa ya fito karara yana tsokaci a kan al'amarin ba.
Domin haka za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa don cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu.
Shekarau yana wannan magana ne a karon farko tun bayan fara takun sakar yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.
"Ita masalaha kamar ciwo ce, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba," in ji Shekarau.
Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta.
Duk da cewa an dan samu sassauci kan bayyanar sabani tsakanin sarki da gwamna, an ci gaba da zaman 'yan marina tsakaninsu, inda kowa yake harkarsa ba tare da shigar da dayan ba.
A watan Mayun bara ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Gwamnati ta ce an kirkiro sababbin masarautun ne domin tabbatar da ci gaba.