Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
BBC ta je garin da cutar Coronavirus ta fara bulla
Latsa wannan hoton domin kallon ziyarar ta BBC
Zuwa yanzu cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutane 80 a China da wasu kasashen duniya, kuma tana cigaba da yaduwa.
Mahukunta sun rufe garin Wuhan inda can ne ta fara bulla kuma tafi tasiri.
Ana tunanin cewa cutar ta samo asali ne daga wata kasuwa da ake sayar da naman namun daji ba bisa ka'ida ba.
BBC ta aike da tawagarta zuwa garin da cutar ta fara bulla.