Vanessa: 'An nuna min wariyar launin fata'

Asalin hoton, Getty Images
Mai fafutukar kare muhalli 'yar kasar Uganda, ta zargi kafafen yada labarai da nuna mata wariyar launin fata bayan cire ta daga wani hoto da aka dauke su da takwarorinta farar fata a Davos.
Vanessa Nakate ta wallafa wani bidiyo mai cike da alhini a shafukan sada zumunta, inda ta ce a karon farko a rayuwarta ta fahimci abin da ake nufi da kalmar ''wariyar launin fata''.
Miss Nakate ta ce kafafen yada labarai da suka hada da na Amurka, da kamfanin dillancin labarai na AP sun cire ta daga jikin hoton.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na AP da tuni ya cire hoton baki daya, ya ce bai yi hakan da wata mummunar manufa ba.
Kamar yadda daraktan daukar hoton AP David Ake ya bayyana, in da yake cewa ''mai daukar hoton yana kokarin samu ainahin girman da ake bukata cikin gaggawa sakamakon kankanin lokacin da yake da shi, don haka ya yi tunanin zai iya cire ginin da ke bayansu.''
''A lokacin da muka koma don kara hotuna a rahoton, kamar yadda muka saba yi a koda yaushe musamman idan muna aikin gaggawa irin wannan, sai muka kara wasu hotunan da aka yanka daban-daban.''
Yaya abin ya faru?
Miss Nakate dai ta halarci babban taron tattalin arziki na duniya a birnin Davos a ranar Juma'a, inda ta halarci taron manema labarai tare da sauran takwarorinta masu fafutuka kan sauyin yanayi wato Greta Thunberg, da Loukina Tille, da Luisa Neubauer da kuma Isabelle Axelsson.
Daga bisani ne ta wallafa wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AP ya wallafa da ya cire ta daga cikin takwarorinta farar fata.
A sanarwar da ta fitar da wani bidiyo, ta zargi kafafen yada labarai da nuna wariyar launin fata.
"Ba mu cancanci a yi mana haka ba mu 'yan Afirka, mu ne muka fi kowa shan bakar wahala sakamakon gurbatar yanayi... Kokarin goge muryoyinmu ba zai sauya komai ba.''
Ta kara da cewa ''Ba na jin dadi, rai na bai min dadi. Wannan duniyar cike take da mugunta.''

Asalin hoton, Getty Images











