Sabuwar dokar bai wa 'yan ci rana damar zama 'yan kasa a India ta janyo rikici

'Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a wasu sassan garin Delhi babban birnin kasar India ,yayin da wasu masu zanga-zanga ke nuna fushinsu game da doka mai cike da takaddama da majalisar dokokin kasar ta amince da ita kan 'yan ci rani.

Sabuwar dokar dai ta bai wa baki da ba musulmi ba kuma suka fito daga kasashen musulmi damar zama 'yan kasa.

Tun bayan da aka amince da dokar dai, al'ummar kasar suka shiga gudanar da zanga-zanga a arewaci da gabashin kasar ta India har ta kai ga 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu gangamin.

Masu gangamin kuma sun cinna wuta kan motocin bas-bas tare da rufe tituna.

Mutane shida ne suka mutu cikin kwanaki biyar din da aka shafe ana gudanar da wannan zanga-zanga.

A karshen makon da ya gabata, masu zanga-zanga a yammacin Bengal sun rufe wasu mahimman hanyoyi yayin da a Assam, gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita da aka sanya domin bai wa mutane damar siyan kayayyakin masarufi na amfanin yau da kullum.

Wannan lamari dai ya sa Amurka da Burtaniya da kuma Canada gargadin matafiya dake son zuwa yankin arewa maso gabashin India inda suka ja kunnan 'yan kasarsu da su zama masu taka-tsan-tsan idan za su ziyarci yankin.

Me ya faru a Delhi?

Dalibai daga fitacciyar jami'ar Jamia Millia Islamia sun gudanar da wani tattaki wanda ya rikide zuwa rikici tsakanin daliban da kuma 'yan sanda.

Kawo yanzu, babu tabbaci kan wanda ya assasa rikicin amma dai an jefa wa 'yan sanda duwatsu inda su kuma jami'an tsaron suka mayar da martani ta hanyar watsa hayaki mai sa hawaye.

Kimanin bas-bas uku da babura da dama ne aka cinna wa wuta.

Daliban jami'ar dai sun nisanta kansu daga zanga-zangar in da wasu 'yan sanda suka bi ta bayan fage suka ce wasu masu tayar da zaune tsaye ne na wurin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hukumar gudanarwar jami'ar ta ce daga baya 'yan sanda sun shiga harabar jami'ar ba tare da izini ba inda suka ci zarafin malamai da kuma dalibai.

'Yan sandan dai sun ce sun yi iya kokarinsu don dakatar da zanga-zangar.

An bukaci makarantun dake kusa da jami'ar a kudancin birnin Delhi da su cigaba da zama a rufe ranar Litinin.

Me ya sa dokar ta jawo rarrabuwar kawuna?

Dokar za ta bai wa mutanen da ba musulmai ba da suka fito daga Bangladesh da Pakistan da kuma Afghanistan, wadanda suka shiga kasar ta India ta barauniyar hanya damar zama 'yan kasa.

Gwamnatin ta India wadda jam'iyyar BJP ta 'yan kabilar Hindu ke jagoranta ta ce dokar za ta yi maraba da mutanen da suka tserewa rikicin addini kariya.

Sai dai kuma masu sharhi suka ce wannan doka wani bangare ne na shirin jam'iyyar BJP, na mayar da Musulmai saniyar-ware.

A farkon makonnan ne ofishin majalisar dinkin duniya dake kula da kare hakkin bil adama ya ce tun asali ta nuna wariya, zargin da gwamnatin ta musanta.

Mutanen yankin Assam dai na ganin bakin da suke shigowa ta iyakokinsu za su iya fin karfinsu anan gaba.