Sabuwar dokar zama dan kasa a Indiya ba ta yi wa Musulmai dadi ba

Gwamnatin India ta tsara wata doka a majalisar dokokin kasar wadda za ta rinka yin afuwa ga bakin haure wadanda ba Musulmai ba da suka je daga makwabtan kasar uku.

Dokar wadda ke cike da ce-ce-ku-ce, na bukatar a samar da izinin zama dan kasa ga tsiraru wadanda ba Musulmai ba a Pakistan da Bangladesh da kuma Afghanistan.

Gwamnatin ta India wadda jam'iyyar BJP ta 'yan kabilar Hindu ke jagoranta, ta ce yin hakan zai ba wa mutanen da suka tserewa rikicin addini kariya.

Tuni dai masu sharhi suka ce wannan doka wani bangare ne na shirin jam'iyyar BJP, na mayar da Musulmai saniyar-ware.

Zartar da kudurin wannan doka, zai zamo wani ma'auni ga jam'iyya mai mulkin India, wadda ke da rinjaye a majalisar wakilan kasar, amma ta ke da rashin rinjaye a majalisar dattawa.

Don haka akwai bukatar dukkanin majalisun kasar biyu su sake yin nazari a kan kudurin dokar.

Tuni dai kudurin dokar ya janyo gagarumar zanga-zanga a bangaren arewa maso gabashin kasar wanda ke da iyaka da kasar Bangladesh, inda mutanen yankin ke ganin bakin da suke shigowa ta iyakokinsu za su iya fin karfin anan gaba.

Me dokar ta kunsa?

Kudurin dokar ya yi gyara ne a kan kudurin dokar da ya haramta wa bakin haure damar kasancewa 'yan kasar India wanda aka yi shi tsawon shekara 64.

A cikin kudurin dokar, an bayyana bakin haure a matsayin baki 'yan wata kasa wadanda suka shiga kasar ba tare da takardar izinin shiga ba, haka kuma an kayyade musu iya lokacin da za su zauna a kasar.

Ita kuwa sabuwar dokar, gyara aka yi a kan ta da inda aka ba wa irin wadannan baki damar zama a kasar har ma da yin aiki a karkashin gwamnatin kasar har zuwa tsawon shekara 11, kafin daga bisani kuma su yi nemi izinin kasancewa 'yan kasa.

Yanzu mutanen da suka fito daga addinai da suka hadar da Hindu da Sikh da Buddhist da Jain da Paris da kuma Kiristanci, idan har daga Pakistan suka fito, to za su iya zama ko aiki a Inida ne har tsawon shekara shida kafin su zama cikakkun 'yan kasa.

Kazalika wadanda su kuma suke da takardar shaidar 'yan kasa ta India da ke zaune a wasu kasashen a 'yanci rani, to zasu iya rasa shaidar zama 'yan kasar idan har suka take wasu dokoki na kasar.

Me yasa dokar take da ce-ce-kuce?

Masu adawa da sabon kudurin dokar, sun ce wannan doka sam ba ta dace ba ta kuma sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

Kundin tsarin mulkin kasar dai ya hana wariyar a kan addini a kan kowanne dan kasa, sannan kuma dukkan 'yan kasar matsayinsu guda.

Wani lauya a kasar Gautam Bhatia, ya ce raba 'yanci rani ta fuskar addini ba abu ne mai alfanu ba.

Da yake kare dokar, wani jagora a jam'iyyar BJP, Ram Madhav, ya ce ba bu wata kasa a fadin duniya ta za ta amince da bakin haure.

Shima da ya ke kare kudurin dokar, R. Jagannathan, editan mujallar Swarajya, ya ce ware musulmai daga cikin dokar zai haifar da gagarumar matsala.

Menene tarihin kudurin dokar?

An fara gyara a kan kudurin dokar zama dan kasa a majalisar dokokin kasar a Yulin 2016.

Dokar ta samu amincewa a majalisar wakilan kasar inda jam'iyyar BJP ke da rinjaye, amma kuma ba ta zama doka ba saboda rashin zartar da ita da majalisar dattawan kasar ta yi bayan zanga-zangar da aka samu a arewa maso gabashin kasar ta India.

Ta yaya rijistar 'yan kasa za ta shafi dokar?

Abubuwan biyu na da alaka sosai, saboda gyaran fuska a dokar zama dan kasar za ta taimakawa wadanda ba muslmai ba wadanda ba sa cikin rijistar.