Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Leicester vs Tottenham: Tottenham ta sha kashi
Kwallon da James Maddison ya dada cikin ragar Paulo Gazzaniga a minti na 85 ce ta bai wa masu masaukin baki Leicester nasara a filin wasa na King Power, inda wasa ya tashi 2-1.
Hakan ya faru ne bayan tauraron dan wasa Harry Kane ya ci kwallon farko a minti na 29 daga kwance bayan sun yi arba da gola Kasper Schmeichael a cikin yadi na 18 - yana daga kwance ya buga kwallon kuma ta wuce cikin raga.
Sai kuma Ricardo Pereira da ya dawo da yaki baya a minti na 69, inda ya farke wa Leicester bayan kwallo ta wuce 'yan bayan Tottenham daga fasin din da Jamie Vardy ya yi masa zuwa cikin yadi 18 daga bangaren hagu.
Tottenham ta zaci wasa ya kare kafin James Maddison ya yi kwance-kwance ya dada kwallo tun daga kusan yadi na 25 zuwa gidan kifinta. Ita ce kwallo ta farko da dan wasan ya ci a Premier ta bana.
Daga bisani Olympiakos ta farke kwallayen kuma wasa ya tashi 2-2.
Kazalika, a ranar 1 ga watan Satumba Tottenham ta barar da kwallo biyu da ta ci Arsenal a filin wasa na Emirate, inda Arsenal din ta farke aka tashi wasa 2-2.