Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko 'yan wasan Najeriya na da inshorar lafiya?
- Marubuci, Daga Juliet Mafua
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen wasanni na BBC Africa, Lagos
Dukkanin 'yan wasan Najeriya za su samu damar samun inshorar lafiya muddin aka samu wani dan majalisa a kasar da ya yi tsayuwar daka kan lamarin.
Ibrahim Olanrewaju ya daukaka wannan batu ga majalisar kasar bayan 'yar wasan Najeriya mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar wato Bidemi Aluko ta sha wahala wajen biyan kudaden magani na cutar cancer da ke damunta.
Olanrewaju dan majalisar tarayya ne mai wakiltar mazabar Aluko da ke jihar Ekiti, ya kuma shaida wa BBC cewa '' Akwai 'yan wasan Najeriya da dama da kullum suke kokarin nemar wa kasar suna.''
''Idan suka bai wa Najeriya wani abu, yakamata ita ma kasar ta ba su wani abu.''
Olanrewaju mai shekaru 45 ya bayyana cewa yana so gwamnatin kasar ta samar da inshorar lafiya ga duk wani dan wasa mai wakiltar Najeriya ba wai lallai sai na kwallon kafa ba.
Karkashin kudirin da ya gabatar gaban majalisar kasar, ma'aikatar harkokin wasanni ta Najeriyar za ta rinka bada wani kaso na tsarin inshorar, inda hukumar inshorar lafiya ta Najeriya wato NHIS za ta biya sauran kason ko da wani dan wasa na bukatar agaji ta fannin lafiya.
A makon da ya gabata ne Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya ta sanar da cewa za ta biya kusan dala dubu 14 domin neman lafiyar Bidemi Aluko mai shekaru 26.
Sanarwar ta zo ne kwana daya bayan sashen BBC na wasanni ya wallafa halin da 'yar wasan ke ciki dangane da rashin lafiyarta.
Tun asali dai likitoci sun gano cewa 'yar wasan na dauke da cutar cancer ta mama, amma daga baya likitoci suka bata damar koma wa domin ci gaba da taka leda bayan shan magunguna da kuma samun sauki.
Amma a watan Janairun wannan shekarar, kwatsam sai cutar ta dawo.
Aluko ta shaida wa BBC cewa ta sayar da duk wani abu da ta mallaka domin kokarin neman lafiyarta.
A watan Yulin bana ne majalisar wakilan kasar ta ce za ta bukaci ma'aikatar lafiya da ta yi dubi dangane da lafiyar Aluko domin samar mata da mafita dangane da lafiyarta.
Amma an ta samun tafiyar hawainiya dangane da wannan batu sakamakon hutun da majalisar kasar ta tafi a wancan lokaci.