Taliban ta mika kai ga Trump

Babban mai shiga tsakani na bangaren Taliban ya yi kira ga Shugaba Trump da a koma bakin tattaunawar neman zaman lafiya kan Afghanistan ta tsakaninsu.

A wata hira ta ba kasafai ba Sher Abbas Mohammad Stanikzai ya ce kawo karshen yakin Afghanistan abu ne mai amfani ga Amurka da Taliban din.

A farkon wannan wata ne kwatsam Shugaba Trump ya soke tattaunawar tsakanin Amurka da Taliban, wadda ake yi a birnin Qatar, inda aka ce an cimma yarjejeniyar ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan din daki-daki.

Kungiyar ta Taliban ta bayyana mamakinta karara kan matakin da Shugaba Trump ya dauka ba zato ba tsammani, na katsewa da kuma watsi da tattaunawar tasu kan batun sasanta rikicin na Afghanistan, a farkon watan nan na Satumba.

Babban mai shiga tsakanin na kungiyar ta Taliban Mohammad Abbas Stanikzai ya shaida wa BBC cewa, bangarorin biyu sun riga sun cimma yarjejeniya, abin da ya rage a lokacin sanya hannu kawai.

Yanzu dai a wannan karon, a wata hira ta ba kasafai ba, wakilin na Taliban ya yi kira ga Shuga Trump da ya sake tura tawagarsa ta tattaunawar a koma a ci gaba da zaman

Ya ce ''Na san akwai masu kamun kafa da sauran mutane da ba sa kaunar samun zaman lafiyar a Afghanistan, saboda suna cin moriya a yakin na Afghanistan. Muna fatan Mista Trump ba zai saurari wadannan mutane ba a ci gaba da yakin a Afghanistan saboda yakin ba shi da amfani garesu haka mu ma ba shi alfanu a garemu.''

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa dole ne sai Taliban ta fito fili ta nuna karara cewa a shirye kuma da gaskiya take son samun zaman lafiyar.

A tattaunawar da BBC Mista Stanikzai ya yi ta musanta zargin cewa Taliban na kai hari kan farar hula, yana mai dora alhakin kashe-kashe da jikkata mutane da ake yi a rikicin a kan dakarun gwamnati.

To sai dai hatta su kansu 'yan kasar ta Afghanistan su ma, kira suke yi ga Taliban din da ta nuna karin alamu da tabbaci na cewa a shirye take don ganin an kawo karshen yakin, wanda a yanzu ake dauka a matsayin mafi hadari a duniya.