Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaba Trump ya yi fatali da yiwuwar sulhu da Taliban
Shugaba Trump ya ce ya soke tattaunawar zaman lafiya da kungiyar Taliban, bayan wani hari da kungiyar ta kai wanda ya hallaka mutum 12, ciki har da sojan Amurka daya, tare da jikkata sama da 40 a Kabul, babban birnin Afghanistan.
A makon da ya wuce Jakadan Amurka a Afghanistan ya cimma daftarin yarjejeniyar sulhu da kungiyar ta masu ikirarin Jihadi, bayan doguwar tattaunawa.
A wani jerin sakon twitter, da ya rika fitarwa, Shugaba Trump ya bayyana daki-daki bayanan wata ganawa ta sirri, da ya shirya yi ranar Lahadi a wurin shakatawa na Camp David.
A wannan zama na sirri, an tsara zai yi zama na keke da keke da shugabannin Taliban, sannan kuma bayan su zai gana daban da shugaban Afghanistan shi ma, a cewar Mista Trump din.
To amma bayan wani wawan hari da kungiyar ta Taliban ta kai a Kabul, babban birnin kasar ta Afghanistan, ranar Alhamis, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha biyun, da suka hada da sojan na Amurka, Shugaba Trump, ya ce, ba tare da wani jinkiri ba ya soke wannan ganawa, bai ma tsaya a nan ba, sai ya kara da watsi da daftarin zaman lafiyar da aka samar tsakanin Amurka da Taliban din.
Yana mai cewa: ''Shin wadanne irin mutane ne wadannan da za su hallaka mutane da yawa haka, kawai domin su karfafa matsayarsu a tattaunawar?''
An dai shafe watanni ana kai gwauro ana kai mari a fagen diflomasiyya, domin samun daftarin yarjejeniyar zaman lafiyar, kafin daga bisani bangarorin biyu su cimma matsaya.
A wani sakon na twitter Mista Trump ya ce idan Taliban ba za ta iya amincewa da dakatar da bude wuta ba a yayin wannan muhimmin zaman sasantawa, to kenan kila ba su da ikon yin wata yarjejeniya mai muhimmanci.
Matakin Mista Trump ya soke wannan ganawa da ya shirya da bangarorin biyu, da watsi da yarjejeniyar da ake yi, wani babban koma-baya ne ga zaman na kusan shekara da aka shafe ana yi a Qatar, wanda aka ce zai kai ga kwashe dakarun Amurka 5,400 cikin mako 20 cikin sati 20 daga Afghanistan.
Ba shakka jami'an diflomasiyyar Amurka ba za su so a ce, abin da suka yi da shugabannin kungiyar ta Taliban, ya tafi a banza ba, an tashi a tutar babu.
Za su yi fatan a farfado da wannan tattaunawa, ba kuma kawai komawa kan teburin ba, a'a, a yi zama na bil-hakki da gaskiya, ba tare da yaudara ko wani mugun nufi ba, don kawo karshen yakin na Afghanistan da Taliban.