Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An cire tallafin mai a Venezuela
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya ce za a kara farashin man fetur da kasarsa ke samarwa dan su yi kai daya da sauran kasashe, hakan shi ya karshen shirin tallafin mai na gwamnatinsa.
Mista Maduro ya ce ya dauki matakin ne saboda masu fasa kwauri na cutar kasar na miliyoyin daloli da ya kamata su zama kudaden shigar gwamnati.
Ita ma Venezuela ta na bai wa 'yan kasar wani kaso a matsayin tallafi, kamar yadda wasu kasashe masu arzikin man fetur ta hanyar saukakawa 'yan kasa farashinsa.
Amma ba su taba kara farashin mai ba, duk kuwa da cewa tattalin arzikin kasar ya dade ya na fuskantar koma baya.
Wakilin BBC a Venezuela ya ce matakin da gwamnati ta dauka katsahan, kokari ne na kara samar da hanyoyin kudaden shiga ga gwamnati dan ceton tattalin arzikin da ya fada halin ni 'ya su.