Za a janyo ruwa daga Congo don raya Tafkin Chadi

Tafkin Chadi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kashi daya cikin goma na ruwan Tafkin Chadi ne kawai ake iya gani a yanzu.

An kammala taron tattauna yadda za a ceto tafkin Chadi daga kafewa, inda taron ya samu halartar wakilan kasashe sama da 30 a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya.

Taron na zuwa a yayin da bayanai suka ce ruwan tafkin ya kafe da kusan kashi 90 cikin 100.

Rayuwar miliyoyin mutane daga kasashen Najeriya da Nijar da Chadi, da kuma Kamaru ta dogara ne a tafkin.

Ana ganin ci gaba da kafewarsa zai iya haifar da matsala a yankin, wanda rikicin Boko Haram ya yi wa mummunar illa.

Kimanin kashi daya cikin goma na ruwan tafkin ne kawai ake iya gani a yanzu, sanadiyyar kafewar da yake yi babu kakkautawa a tsawon shekaru.

Mutane da dama a yankin na cikin fargaba, domin nan gaba kadan al'amura za su iya tsayawa cak, matukar ba a dauki kwakkwaran mataki cikin hanzari ba.

Kuma kafewar tafkin ya haifar da rashin ayyukan yi ga mutanen da ke dogaro da tafkin domin samun abinci.

Daga cikin matakan da ake tunanin za a dauka domin ceto tafkin shi ne janyo ruwa daga kasar Congo.

Sai dai kuma wadanda matsalar ta shafa kai-tsaye na ganin za su iya shiga mawuyacin hali kafin fara aiwatar da shirin yanjo ruwan daga Congo.

Abubakar Gamandi shugaban kungiyar masunta na Tafkin Chadi, wanda kuma ya halarci taron a Abuja ya shaidawa BBC cewa "Abin da muke tsoro shi ne kafin a waiwayo aikin raya tafkin bayan an watse taron."

Ya ce sauran kifin da ya rage a ruwan tafkin na iya karewa idan har ba a gaggauta aiwatar da matakan da aka yi alkawali ba a taron.

Akalla dai, kimanin mutane miliyan 40 ne tafkin ke samar wa ruwa na amfanin yau da kullum.

Haka ma sana'o'i irin noman rani da kamun kifi, da kuma shayar da dabbobi.

Tafkin Chadi

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai kuma, bushewa da tafkin ke yi a kowace safiyar Allah na haifar da kaurar al'umma zuwa wasu yankunan na daban, musamman ma makiyaya da ke nema wa dabbobinsu abinci.

Injiniya Hussaini Adamu Ministan ruwa na Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka halarci taron ya ce za a samo ruwan da za su cika tafkin, kuma batun yanyo ruwan daga Congo ne aka ba muhimmanci.

Sai dai ana ganin za a shafe shekaru kafin kammala aikin raya tafkin, lamarin da wasu ke ganin an makara.

A wani rahoto da Hukumar hukumar abinci ta duniya wato FAO ta fitar a 2017 ta ce mutane fiye da miliyan bakwai ke fuskantar barazanar Yunwa, a tafkin Chadi.

Hukumar ta ce mutane na bukatar taimakon gaggawa na abinci da ma sauran abubuwan more rayuwa.

Tun dai a bara ne kjasashen duniya suka yi alkawalin tara dala miliyan 670 don taimakon gaggawa ga al'ummar yankin tafkin Chadi, wanda ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.