Akwai yiwuwar samun mai a tafkin Chadi - NNPC

Asalin hoton, NNPC Website
Kamfanin mai na NNPC a Nigeria, ya ce akwai yiwuwar samun mai a yankin tekun Chadi inda rikicin Boko Haram ya daidaita.
Manajan Daraktan kamfanin Ibe Kachikwu ya ce bayan daukar lokaci mai tsaho ana lalube cikin duhu kan yiwuwar samun man a yankin tafkin Chadi, a yanzu kam akwai kwarin gwiwar haka za ta cimma ruwa.
Mr Kachikwu wanda ya zama shugaban NNPC a watan Agustan da ya wuce, ya ce wannan wata gagarumar nasara ce da ke nuna akwai dimbin danyen mai dankare a arewacin Nigeria.
A ranar lahadi ne aka ambato Mr Kachikwu na cewa kafin karshen shekarar nan za a samu labari mai dadi kan wannan batu.
Sai dai bai yi wani karin bayani ba, amma ana ganin cewa yana magana ne a kan yankin Kukawa da ke jihar Borno inda suke fuskantar ta yar da kayar bayan kungiyar Boko Haram kusan shekaru shida.






