'Yan cirani 31 sun nutse a tekun Libya

An kai gawawwakin mutane sansanin sojin ruwa na Libya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kai gawawwakin mutane sansanin sojin ruwa na Libya

'Yan cirani 31 ne suka nutse a cikin teku bayan da jirgin ruwan da suke ciki, ya kife a gabar tekun Libya a ranar Asabar.

Mutanen da abin ya rutsa da su suna kokarin ketarawa ne zuwa nahiyar Turai daga tekun baharum.

Kuma akwai yaara kanana na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

A ceto mutane 60 daga cikin ruwa kuma daga bisani an ceto 140 daga cikin wani jirgin ruwa.

Kyawon yanayi ya sa an samu karuwa a yawan 'yan cirani da ke tafiya zuwa Turai daga Libya a kwanakin baya bayanan.

Masu tsaron gabar teku a Libya sun ceto mutum 250 a ranar Alhamis.

Haka zalika kuma masu sintiri a tekun Italiya sun ce sun ceto mutane 1,100 a ranar Talata.

Kwale-kwalen ya ci karo ne a gabar birnin Garaboulli, mai nisan kilomita 60 daga birnin Tripoli.