'Yan cirani 31 sun nutse a tekun Libya

'Yan cirani 31 ne suka nutse a cikin teku bayan da jirgin ruwan da suke ciki, ya kife a gabar tekun Libya a ranar Asabar.

Mutanen da abin ya rutsa da su suna kokarin ketarawa ne zuwa nahiyar Turai daga tekun baharum.

Kuma akwai yaara kanana na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

A ceto mutane 60 daga cikin ruwa kuma daga bisani an ceto 140 daga cikin wani jirgin ruwa.

Kyawon yanayi ya sa an samu karuwa a yawan 'yan cirani da ke tafiya zuwa Turai daga Libya a kwanakin baya bayanan.

Masu tsaron gabar teku a Libya sun ceto mutum 250 a ranar Alhamis.

Haka zalika kuma masu sintiri a tekun Italiya sun ce sun ceto mutane 1,100 a ranar Talata.

Kwale-kwalen ya ci karo ne a gabar birnin Garaboulli, mai nisan kilomita 60 daga birnin Tripoli.