Nigeria: Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Lagos

Nigeria Train

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya dai tana kokarin farfado da layukan dogonta

A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya.

Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar jiragen kasa ta Najeriya da ke da hedikwata a Legas, Yakubu Mahmud, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela da take kokarin tsayawa ta daki jirgin kasan.

Jirgin dai ya taso ne daga yankin Ijoko zai tafi yankin Ido da suke cikin birnin Lagos din.

Jami'in ya ce wadanda suka rasa rayukansu suna cikin wadanda suka fado daga bakin kofar jirgin.

Wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka mutu ya karu domin akwai mutane da dama da suka ji munanan raunuka.

Hatsarin layin dogo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba kasafai ake samun hatsarin layin dogo a Najeriya ba

Ba a dai cika samun hatsarin jirgin kasa a Najeriya ba kamar su Indiya inda aka fi amfani da layin dogon.

Karanta karin wasu labaran: