Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Carlo Ancelotti ya dauki Champions League hudu a tarihin gasar
Carlo Ancelotti ya zama koci na farko da ya lashe Champions League guda hudu a tarihin gasar.
Ranar Asabar Real Madrid ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a karawar da suka yi a Faransa, inda ta lashe Champions League na 14 jumulla.
Vinicius Junior ne ya ci kwallon tilo da ya bai wa kungiyar damar lashe kofin Zakarun Turai na bana, bayan da ta ci La Liga na kakar nan kuma na 35 jumulla.
Ancelotti dan kasar Italiya ya zama na farko da ya dauki Champions League hudu a matakin koci, bayan Bob Paisley da kuma Zinedine Zidane, wadanda kowanne ya lashe sau uku-uku.
Haka kuma dan kasar Italiya shi ne kan gaba da ya je wasan karshe karo biyar, ya dauki biyu a Real Madrid da biyu a AC Milan.
Ya fara cin kofin a Real Madrid a 2014 a Lisbon a kakar farko da ya fara jan ragama, inda Real ta doke Atletico Madrid 4-1.
Karon farko da ya fara daga kofin shi ne a AC Milan a 2003 a Old Trafford, inda suka yi nasara a kan Juventus a bugun fenariri, sannan ya dauki na biyu a 2007, bayan doke Liverpool 2-1 a Athens.
A Real Madrid kuwa ya lashe Champions League a 2012 da kuma 2022.
Ancelotti ya shiga jerin kociyoyin Real Madrid da suka dauki Champions League fiye da daya a kungiyar da suka hada da Zidane mai uku da Villalonga mai biyu da kuma Carniglia.
Sauran sun hada da Miguel Muñoz da Del Bosque da kuma Heynckes, wanda ya dauki kofi na bakwai.