Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Kamaru: Masoya ƙwallon ƙafar da ba sa son ƙasarsu ta yi nasara
Gasar cin Kofin Ƙasashen Afirka da aka yi ta baya-bayan nan a Kamaru ya nuna yadda mutane ke ƙaunar ƙwallon ƙafa, amma yayin da ƙasar ke shirin buga wasannin cancantar shiga Kfoin Duniya na 2022, ba duka 'yan Kamaru ne ke son ƙasar ta yi nasarar zuwa ba gasar ba, kamar yadda Tony Vinyoh ya ruwaito.
Abu ne sananne cewa bai kamata a haɗa siyasa da wasanni ba, amma idan ana maganar ƙwallon ƙafa a Kamaru abubuwan biyu a haɗe suke.
Rikcin shekara biyar tsakanin 'yan aware na ɓangaren rainon Ingila da kuma gwamnatin ƙasar ya zarce zuwa filin wasa.
Lokacin da Masar ta doke Kamaru a wasan kusa da na ƙarshe a gasar ta Afcon, kusan duka ƙasar ta shiga makoki amma ban da yankin Bamenda - inda nan ce cibiyar adawa a yankin rainon Ingila - sun ɓarke da murna.
Aka dinga busa usur tare da ife-ife, har ma da masu wasa da babura a garin Bambili, abin da ke nuna irin abin da 'yan kudancin ƙasar ke ji game da tawagar ƙasar da ake kira Indomitable Lions, wadda wasu ke kallo a matsayin ta haɗin kan ƙasa amma ban da su.
Dagacikin m asu murnar doke Kamaru akwai Dr Ngwa Ebogo, wani likitan tiyata a ɓangaren mafitsara.
A matsayinsa na mai son ƙwallon ƙafa, yana sane da rawar da wasanni ke takawa a siyasa a ƙasar da kuma tasirinta a kan marasa lafiyar da yake kula da su.
"Wannan ƙasar tana iya amfani da wasanni don ɓoye batutuwan da ke damun al'umma. Za su iya zuba kuɗi a harkar ƙwallon ƙafa saboda sun san tana haɗa ƙan al'umma," a cewarsa.
Ɓacin ran da aka nuna yanzu akasi ne na abin da ya faru a 1998 lokacin da mazauna Bamenda suka cinna wa ofishin kamfanin lantarki na ƙasar wuta saboda na ɗuke wuta ana daf da take wasa tsakanin Kamaru da Austria a gasar Kofin Duniya na shekarar.
Dr Ebogo ya goyi bayan Kamaru har zuwa 2016 lokacin da rikicin kudancin Kamarun ya fara. Yanzu ya yi imanin cewa nasarar da tawagar ka samu riba ce ga gwamnati wajen shirinta na kawar da hankalin 'yan ƙasa.
"Ko da a ce kana tsaka da gwagwarmaya sai Kamaru ta yi nasara, sai ka manta ma abin da kake gwagwarmayar a kai. Sun daɗe sun aikata hakan. Duk sanda 'yan wasan suka yi nasara ƙarin wahala ce kan al'umma."
Tawagar na taka muhimmiyar rawa a tsarin da Shugaban Ƙasa Paul Biya mai shekara 89, wanda ke cika shekara 40 a lkan mulki.
"Mafi yawan 'yan Kamaru na tunanin idan Kamaru ta ci wasa saboda shugaban ƙasar ne," in ji Dr Ebogo.
"Idan tawagar ta samu nasara sai ka ji mutane na yi wa shugaban murna."
Sai dai mazauna Bamenda na taka-tsantsan game da wanda suke faɗa wa ra'yoyinsu, saboda gwagwarmaya ce ta kullum da suke yi wajen ɓoye fushinsu idan tawagar ta yi rashin nasara.
A lokacin mulkin mallaka, Faransa da Birtaniya ne suka mallake ta Kamaru, abin da ya sa suka bar al'adunsu da harsunansu a ƙasar.
Tsawon shekaru bayan samun 'yancin kanta, mazauna kudancin ƙasar na ganin ana zaluntarsu ta hanyar raba su da mulki da kuma harkokin tattalin arziki a hannun masu magana da harshen Faransanci mafiya rinjaye.
Abin ya zama babban rikici da kuma kiraye-kirayen neman samun 'yancin kai ga yankin rainon Ingilan.
Waɗanda lamarin ya fara shafa su ne tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar.
'Ko ma wane ne ban da Kamaru'
Lokacin da Kamaru ke karɓar bakuncin gasar mata ta Kofin Ƙasashen Afirka a 2016, za ta kara ne da Najeriya.
Bayan fara gasar a ranar 19 ga watan Nuwamba, akasarin wuraren shaƙatawar Bamenda sun cika da mutane na sowa da ihun goyon bayan 'yan matan Kamaru duk da rashin imanin da jami'an tsaro suka gwada wa masu zanga-zanga a yankin 'yan makonni kafin haka.
Amma kafin haka, sai murna ta sauya zuwa baƙin ciki.
Da yawan mazauna yankin ba su yi wani shiri ba kafin fara gasar Afcon da aka gama kwanan nan. Da yawansu kan ce kowa ya yi nasara ban da Kamaru. Dr Ebogo ma na da irin wannan ra'ayi kuma ya shafe lokaci yana kai ziyara sansanin abokan karawar Kamarun.
"A Bamenda babu wani abu da ke nunan ana gasar Afcon. Sun yi ta so su ɗauki mutane zuwa filin wasa na Bafoussam amma ba wanda ya bi su," a cewarsa yana magana kan tikitin kyauta da aka raba wa mutane da kuma tilasta wa mutane zuwa kallon wasannin.