Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Yadda 'yan Kamaru masu masaukin baƙi suka ji da rashin nasara a gasar Afcon
Latsa hoton sama ku kalli bidiyon:
Wasu mazauna Kamaru mai masaukin baƙi a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta Afcon 2021 sun bayyana wa BBC Hausa halin da suka shiga bayan doke tawagar ƙasar da Masar ta yi a wasansu na yammacin Alhamis.
Bayan shafe minti 90 ana gumurzu, babu wanda ya yi nasara. Aalkalin wasa ya kara minti 30, inda a nan ma ba a samu wanda ya yi nasara ba har sai da aka je ga bugun fanareti.
A nan ne Masar ta doke Kamarun da ci 3-1.
Yanzu dai Masar za ta buga wasan ƙarshe da Senegal ranar Lahadi.
Golan Masar, Gabaski, ya yi kokari ta hanyar kaɗe ƙwallo biyu, yayin da daya ta tsallaka saman raga.