Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar Kwallon Kafar Afirka: Wasan kwallon da ya gamu da bala'i
A jerin wasikunmu da muke gabatar muku daga marubutun Afirka, a wannan karon dan jarida mai rubut labaran wasanni dan kasar Kanada dan asalin Aljeriya, Maher Mezahi, wanda ya je Kamaru domin halartar gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka, ya yi nazari kan yadda ya samu kansa cikin halin murna da kuma takaici game da gasar, sakamakon mutuwar 'yan kallo a wurin shiga filin wasa.
A lokacin da aka neme ni da na yi rubutu a game da yadda na ga gasar ta Afirka a Kamaru, abin da ya zo min zuciyata shi ne na fito da jerin abubuwan da suka sa gasar ta bambanta da sauran manyan gasar kwallon kafa.
Abin da ke raina shi ne na kwarzanta kwallon kafar Afirka.
Domin ko ba komai gasar cin kofin Afirka, Afcon, gasa ce da kowa a Afirka da ma wadanda suke da alaka da al'adu da nahiyar Afirka ke so.
Gasar farko a 1957 da kuma wadda aka yi a 1959, an yi su ne a matsayin wata hanya ta yaki da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu
'Yan wasa da 'yan jarida da 'yan kallo kowa na kallon gasar ta Afirka a matsayin ainihin manufa ta wasan kwallon kafa, ba kamar yadda wasu wasannin gasar da ake yi ba a wasu wuraren wadanda ma ake tsara su fiye da wannan.
Akwai kuma yanayi na nishadi da abokantaka da kuma alfahari da gasar ta Afirka ke sanyawa a dukkanin kasashen nahiyar.
Gasa ce ta magoya baya na musamman
Daga cikin kyawawan abubuwan da suke a gasar akwai tsarin bin dokokin yaki da cutar korona, wadanda suka hada da daukar hoton kirjin mutum.
Wadannan na daga matakai masu tsanani da aka taba dauka a wasan kwallon kafa, domin kare aukuwar wata matsala ta lafiya.
A duk lokacin wannan gasa ta shekara bibbiyu ana iya ganin magoya baya da kan yi shiga iri daban-daban ta musamman a cikin 'yan kallo.
Dauki misalin dan Tunisiya mai zanen giwa da fentin tutar kasar a jikinsa, ''Reda The Elephant'' wanda kusan ya fi kowa iya murnar cin kwallo, ko kuma dan Ivory Coast ''Petit Bamba'', wanda ke jagorantar magoya bayan tawagar kasarsa a rawar da suke yi lokacin wasanninsu, dukkanin wadannan ba karamin nishadi da kayatarwa suke sanyawa gasar ba.
Wani dan jarida mai zaman kansa dan kasar Italiya, Alex Cizmic, wanda yake halartar gasar, yana cike da nishadi inda yake cewa, ''Yanayi ne na nishadi tsantsa.''
Ya tuna da gasar da ya taba halarta a baya, ya ce: "A 2019 a Masar, na samu damar halartar atisayen tawagar 'yan wasan Uganda inda na tattauna da tauraroron dan wasan gabansu Farouk Miya, wanda ban taba haduwa da shi ba.''
Ya ce ''Nan da nan na dauki waya na kira tsohon kociyansa, Milutin Sredojevicm wanda dama ina magana da shi, na hada tattaunawa a tsakaninsu. Abin gwanin ban sha'awa.''
Su ma kananan kasashe suna haskakawa.
Gambia da Komoros (Comoros) ba su taba zuwa gasar ba sai a wannan karon, kuma lalle ba shakka sun taka rawar gani. Sun sa kasashensu alfahari.
Kafin Gambia ta yi wasnta na farko da Mauritania, na nemi wani dan kasar ta Gambia da y rubuta min yadda yake ji, a daidai lokacin da ake rera taken kasar tasa.
"Ina cike da alfahari da shaukin kaunar kasata, jin ana rera taken kasata a karon farko a gasar Afirka,'' in ji shi.
Ya kara da cewa a lokacin da muka ci kwallon farko, na kasa yin komai. Amma can a zuciyata ina cike da murna da alfahri na san abin da wannan kwallo za ta yi ga al'ummar kasata. Ta hada kan al'ummar.''
Takalma a warwatse
To amma kash! A lokaci daya da wani yammaci duka wadannan abubuwa na jin dadi da nishadi game da gasar ta Afirka, wani abin takaici ya gitta ya kuma mamaye ta.
A yayin da mai masaukin baki Kamaru ke shirin yin wasanta na zagaye na biyu da Komoros (Comoros) a sabon filin wasa na Olembé a babban birnin kasar, Yaoundé, hargowa ta fara haduwa a wajen filin.
Da misalin karfe bakwai da rabi na yamma (agogon kasar), minti talatin kawi ya rage kafin a take kwallo, sai turmutsutsun dubban 'yan kallo da ke waje ya barke, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takws, wadand suka hada da yaro dan shekara takwas, in ji hukumomin Kamaru.
Na je fili wasan da wuri, tun da rana, to amma tun sa'o'i kafin a fara wasan, matakn da aka dauka na kare dubban 'yan kallo abin takaici ne.
Na halarci kasashe bakwai domin kallon wasannin kasashen Afirka kuma a kodayaushe, ina lura da wani abu guda daya: za ka ga tarin 'yan sanda amma kuma matakan kare lafiyar jama'a ba su da yawa.
Abin mamaki ne da takaici a ce a filin wasan da yake daukar mutane dubu 60, 'yan jarida da magoya baya da kusan kowa, wadanda da manyan baki ba ne suna shiga ta kofa daya.
Gwajin cutar korona da kuma tantance mutane domin yi musu allurar riga-kafin ya kara haifar da jinkiri wajen shiga filin wasan.
Ban san abin da ya faru ba sai da wani abokin aiki ya zungure ni ya min rada cewa: ''Akwai fa matsala a waje.''
Nan da na muka garzaya waje, amma ba mu ga komai ba.
Abin da muka gani kawai shi ne 'yan takalma a warwatse da 'yan tsummokara na tufafi da suka yage a kasa.
Bayan 'yan mintina sai labari ya rika bayyana na rade-radin mutuwa.
A dakin manema labarai, sai 'yan jarida suka rika musayar jerin sunayen wadanda abin ya rutsa da su da kuma hotunan bidiyo na turmutsutsun.
Washegari sai hukumar kwallon kafa ta Afirka ta fitar da sanrwa inda a ciki ta ce ta dauki nauyin abin da ya faru tare da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu.
To amma ba a dage wasanni ba. Kuma aka ci gaba da gasar.
A ganina bai kamata a ce an yi wasa ranar Talata, washegarin da abin ya faru ba. Saboda kamar ba a mutunta iyalan da suka rasa 'yan uwansu ba, kuma duk wanda ke da alaka da gasar na kokarin ya san yadda abin da ya faru.
Kusan a ce wannan ba lokaci ba ne da za a yi magana ko murnar wasan kwallon kafa ba.