Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Turmutsutsu ya yi ajalin mutane a filin wasa a Kamaru
Aƙalla mutum takwas aka bayar da rahoton sun mutu sannan 38 sun samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu da ya auku a wajen filin da ake buga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta Afcon a Kamaru.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda 'yan kallo suka rinƙa kokawar shiga filin wasa na Paul Biya da ke birnin Yaounde.
Naseri Paul Biya, gwamnan yankin Tsakiyar Kamaru, ya ce akwai yiwuwar a samu karin mutanen da abin ya shafa, a cewar kamfanin labarai na AP.
Wani rahoton kuma na cewa akwai yara da dama da suka suma.
Filin wasan na iya daukar mutum dubu 60, amma saboda matakan da ake ɗauka saboda annobar korona ba a yarda a haura kashi 80 cikin 100 na wannan adadin ba.
Jami'ai sun ce mutum dubu 50 ne suka yi kokarin shiga filin wasan domin kallo.
Ma'aikaciyar jinya Olinga Prudence ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa wasu daga cikin mutanen da suka jikkata na cikin yanayi na galabaita.
Hukumar kwallon kasashen Afirka, CAF, a wata sanarwa ta ce tana bincike kan lamarin domin samun ƙarin bayanai kan ainihin abin da ya faru.
An fafata a zagaye na biyu na gasar tsakanin Kamaru da Comoros duk da faruwar wannan al'amari, kuma mai karbar bakwancin wasan ta yi nasara da 2-1.