Mauricio Pochettino 'bai taba cewa zai bar' ba PSG, in ji Leonardo

Mauricio Pochettino zai ci gaba da kasancewa a matsayin kocin Paris St-Germain kuma "bai taba cewa zai tafi ba" a yayin da ake rade-radin zai tafi Manchester United, in ji daraktan wasanni na kungiyar Leonardo.

Kwangilar Pochettinoa PSG za ta kare a a shekarar 2023, kuma yana cikin wadanda ake tunanin za su maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a Old Trafford.

"Ba ma son Pochettino ya tafi," in ji Leonardo.

"Bai taba cewa zai bar kulob din ba kuma babu kulob din da ya tuntube mu."

Leonado ya kuma ba su tuntubi Zinadine Zidane ba domin zama koci a PSG.

Manchester United na gab da daukar koci dan kasar Jamus Ralf Rangnick a matsayin.

United ta mayar da hankali wajen daukar kocin rikon kwarya domin maye gurbin Solskjaer, wanda aka kora daga aiki ranar Lahadi bayan sun sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 a gasar Firimiya.