Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta kai zagayen karshe a neman zuwa kofin duniya
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta kai zagaye na uku a shiyyar nahiyar Afirka a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Super Eagles ta tashi 1-1 da Cape Verde a karawar da suka yi a filin wasa na Teslim Balogun a jihar Legas, Najeriya ranar Talata.
Super Eagles ce ta fara cin kwallo ta hannun Victor Osimhen a minti daya da fara wasa, sai dai kuma minti hudu tsakani Cape Verde ta farke ta hannun Stopira.
Tawagogin sun kara ranar 7 ga watan Satumba a wasan farko a rukuni na uku, inda Najeriya ta je ta yi nasara da ci 2-1.
Cape Verde ce ta fara cin kwallo ta hannun Dylan Tavares a minti na 19 da fara tamaula daga baya Super Eagles ta farke ta hannun Victor Osimhen, sannan Kenny Rocha Santos ya ci gida saura minti 14 a tashi daga fafatawar.
Ita kuwa Liberia doke Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta yi da ci 3-1 a daya karawar ta rukuni na ukun ranar Talata.
Ta kuma ci kwallo biyu a raga ta hannun Peter Wilson da kuma Marcus Macauley, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta zare daya ta hannun Isaac Ngoma.
Da wannan sakamakon Super Eagles ta ja ragamar rukuni na uku da maki 13 bayan buga wasa shida-shida, yayin da Cape Verde ta yi ta biyu da maki 11.
Liberia ce ta uku da maki shida da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya mai maki hudu ta karshen teburi.
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf za ta raba kasashen da suka kai bantensu zuwa wasannin da suka buga don fitar da biyar din za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.