Steven Gerrard ya zama kocin Aston Villa

Steven Gerard

Asalin hoton, Getty Images

Aston Villa ta nada Steven Gerrard a matakin sabon kociyanta, kan yarjejeniyar kaka uku da rabi.

Hakan ya kawo karshen kaka ukun da ya ja ragamar Rangers mai buga gasar Scotland.

Gerrard ya maye gurbin Dean Smith, wanda ta sallama ranar Lahadi, bayan da aka doke kungiyar wasa biyar a jere a gasar Premier League.

Villa tana ta 16 a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da ta ukun karshe.

Gerrarrd ya fara aikin koci a babbar kungiya a gasar Scotland da Rangers tun daga 2018 ya kuma bar wasannin tana mataki na daya da tazarar maki hudu tsakaninta da Celtic abokiyar hamayya.

Ya buga wa Liverpool wasa 710 da lashe kofi tara daga nan ya koma gasar Amurka a kungiyar LA Galaxy a 2015, sannan shekara daya tsakani ya yi ritaya.

Ya kuma horar da matasan Liverpool daga nan ya ja ragamar matasa 'yan kasa da shekara 18 na kungiyar tsakanin 2017-18.

Gerrrard shine na hudu a yawan buga wa tawagar Ingila tamaula mai wasaa 114 da cin kwallo 21.