Barcelona ta gabatar da Xavi Hernandez gaban magoya baya

Asalin hoton, Getty Images
Xavi Hernandez zai fara jan ragamar atisayen Barcelona ranar Talata, bayan da aka gabatar da shi gaban magoya baya ran Litinin a matakin sabon koci.
Zai fara gudanar da aikin a Camp Nou ba tare da fitattun 'yan wasan kungiyar ba, wadanda suka je buga wa tawagoginsu wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya.
Cikin jerin 'yan wasan da aka gayyata daga Baraca sun hada da Jordi Alba da Sergio Busquets da kuma Gavi daga Sifaiya da Philippe Coutinho daga Brazil da Ronald Araujo daga Uruguay.
Sauran sun hada da Ter Stegen daga Jamus da Frenkie de Jong da kuma Memphis Depay daga Holland da Clément Lenglet daga Faransa da kuma Yusuf Demir daga Austria.
Da zarar an kammala wasannin neman gurbin cin kofin duniya, Xavi zai fara jan ragamar Baracelona wasan hamayya da za ta buga da Espanyol ranar 20 ga watan Nuwamba a gasar La Liga.
Barcelona ta gabatar da Xavi a gaban magoya bayanta da kuma 'yan jarida a Nou Camp, wanda ya maye gurbin Ronald Koeman da ta sallama.
Tuni dai Xavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2024.
Dan kasar Sifaniya mai shekara 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga 2019, wanda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona ranar Juma'a.
Barcelona ta sanar cewa Xavi zai horar da kungiyar zuwa karshen kakar bana daga nan ya kara kaka biyu a gaba.
Xavi, wanda ya yi wa Barca karawa 767 a kungiyar ya lashe kofi 25 a shekara 17 da ya yi a Camp Nou,
Daga nan ya koma Al Sadd a matakin dan wasa a 2015, sannan ya zama kocinta.
Ya kuma karbi aikin horar da kungiyar Qatar a 2019, wanda ya lashe kofin lik din a bara, kuma kungiyar ta yi karawa 36 a Lik din ba a doke ta ba.
Tun bayan da Barcelona ta kori Ronald Koeman ranar 27 ga watan Oktoba ake alakanta shi da aikin.
Barcelona tana ta tara a teburin La Liga, bayan da ta ci kwallo uku ranar Asabar a gidan Celta daga baya aka farke ta tashi 3-3 a wasan mako na 13 a gasar Sifaniyar.
Yadda aka yi bikin gabatar da Xavi ranar Litinin:
11.30 na safe aka bude kofofin filin wasa na Camp Nou.
1.00 na rana aka gabatar da Xavi Hernandez a matakin sabon kocin kungiyar Barca a tsakiyar filin Camp Nou.
1.30 na rana Xavi Hernandez ya yi hira da 'yan jarida











